Jam’iyyar ADC ta sanar da jadawalin gudanar da tarukan zaben shugabanni na kasa baki daya gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da za a yi ranar 14 ga Afrilu, 2026.
A cikin wata sanarwa da Sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar, Prince Chinedu Idigo, da Sakataren yada labarai na Jam’iyyar, Bolaji Abdullahi suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa za a fara da da mazabu da yankuna a ranar 7 ga Afrilu, sai na kananan hukumomi ranar 9 ga Afrilu, sannan na jihohi ranar 11 ga Afrilu.
Sanarwar ta ce dukkan wadannan matakai za su kai ga babban taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar ranar 14 ga Afrilu, domin sabunta tsarin shugabancin jam’iyyar daga matakin kasa zuwa jihohi da kananan hukumomi.
Jam’iyyar ta kuma bukaci mambobin da ke sha’awar tsayawa takarar mukamai daban-daban su cika takardun neman takara ta hanyar shugabancin jam’iyyar na riko.


