Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

OECD 2024 raporuna göre, Avrupa’daki lisanssız bahis sitelerinin oranı %35’tir; bu, bettilt giriş gibi lisanslı sitelerin önemini artırır.

bahsegel bahsegel giriş bahsegel bettilt bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş paribahis

Dijital ortamda oyun keyfini artıran https://paribahis-resmi.ink/ kategorileri öne çıkıyor.

bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bettilt bettilt güncel giriş
HomeLabariA kan wayar...

A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa

Matashi a garin Gashuwa ta jihar Yobe, mai suna Umar Aminu Ahmad, wanda aka fi sani da Umar Ɗan Paleti, ya ɗauki buhun shinkafa a kansa, mai nauyin kilogram 100 inda ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, don ya ci gasar wayar Android da suka yi.

Wannan lamari ya faru ne a jiya Jumu’a, a unguwar Tsamiya, Zangon Takari. Inda matasan suka yi gasa a kan duk wanda ya ɗauki buhun shinkafa mai nauyin kilogram 100, daga Zangon Takari zuwa Kara (sabuwar kasuwar ‘yan shinkafa), a cikin garin Gashuwa, to zai ba da wayarsa ta Android. Nan take Umar ya ce zai iya, shi ma Umar ya saka wayarsa, a kan idan bai kai ba, shi ma ya ba da wayarsa.

Ku kuma karanta: Katin shedar ɗan ƙasa ya fallasa kwamandojin Boko Haram 7 da suka dawo daga aikin Hajji – Minista

Aka ɗauko buhun shinkafa aka ɗora masa, tun daga Zangon Takari, har zuwa Kara, Umar ya kawo buhun shinkafar nan bai tsaya ba. Nan take aka ba shi waya ƙirar Android da aka yi gasa akai.

A wani faifayin ‘video’ da Neptune Prime ta samu, wanda Assalafy Multimedia take tattauna wa Umar ɗin, ya tabbatar da cewa lallai ya ɗauki buhun shinkafa ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, bisa gasa da suka yi a tsakanin su, kuma ya ci wayar Android.

Da ake tambayarsa, kan cewa bayan wayar Android an ba shi dubu 100, sai Umar yace “Ni ba wanda ya ba ni dubu 100. Iya waya ce muka yi gasa a kanta, kuma ita aka ba ni. Sai dai a hanya ta tafiya, mutane sun yi ta jinjina min, wasu suna ba ni kuɗi, kuma hakan shi ne ya ƙara min ƙarfin gwiwa da kuzari har na yi nasara a wannan gasar.

“Lallai ni ban taɓa yin sana’ar dako ba, kawai dai na ga zan iya ne, shi ya sa na yi” inji Umar

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Zargin cin zarafi: Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura

Zargin cin zarafi: Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, sakamakon zargin cin zarafin wata mata ‘yar ƙasar waje da ake dangantawa da...

Harshen Hausa a Zamanin Fasahar AI

HARSHEN HAUSA A ZAMANIN FASAHAR AI Daga Yusuf Lawan Nasidi A da, samun wasu ayyukan fasaha na buƙatar lokaci da kuɗi da kuma neman ƙwararrun mutane. Idan mutum yana son rubuta littafi, ko ya yi zane, ko ya shirya gabatarwa, ko...

Ya Kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci Ya Zurfafa Tunani da Ƙwarewa Wajen Haɓaka Harkokin Isar da Saƙo — Dr. Hassan Gimba

Ya Kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci Ya Zurfafa Tunani da Ƙwarewa Wajen Haɓaka Harkokin Isar da Saƙo — Dr. Hassan Gimba Taron Makon Yaɗa Labaran Harkar Musulunci, wanda ke gudana da taken “Ƙarfafa Ƙwarewar Yaɗa Labarai Domin Isar da...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.