Connect with us

Labarai

Ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS ya nemi a cire wa Nijar takunkumi

Published

on

Ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ranar Laraba ya yi ƙira a cire takunkuman da aka sanya wa ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulki gabanin wani muhimmin taro na gaggawa da shugabannin ƙungiyar za su yi.

Ƙungiyar ECOWAS ta faɗa cikin rikici bayan a watan jiya ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun bayyana ficewa daga cikinta.

Kazalika ƙungiyar tana ƙoƙarin shawo kan wani sabon rikicin siyasa da ya ɓarke a Senegal bayan Shugaba Macky Sall ya ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar a watan nan na Fabrairu zuwa Disamba.

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon, wanda ya jagoranci ƙasar wajen yaƙin basasa da ƴan a-waren Biafra daga 1967-70, ya yi gargaɗi cewar “rashin haɗin-kai” na barazana ga ECOWAS.

Ya yi ƙira ga shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su duba yiwuwar “cire dukkan takunkuman da aka sanya wa Burkina Faso, Guinea, Mali da Nijar”.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta gaza biyan bashin da ya kai dala miliyan ɗari biyar – WAEMU

A wani taro da ECOWAS ta gudanar a Abuja, Janar Gowon ya yi ƙira ga shugabannin mulkin sojin Burkina Faso, Mali da Nijar su janye aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.

Ya roƙe su cewa “Don girman Allah ku dawo.”

Ƙasashen uku na cikin waɗanda suka kafa ECOWAS a 1975, amma ƙungiyar ta dakatar da su daga cikinta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatocin fararen-hular ƙasashen.

ECOWAS ta sanya takunkumai masu tsauri a kan Mali da Nijar, matakin da ya harzuƙa sojojin da ke mulki.

Ranar Litinin, sojojin da ke mulki a Guinea, waɗanda suka ƙwace mulki a watan Satumba na 2021, sun rusa gwamnatin ƙasar.

Janar Gowon, mai shekara 89, dattijo ne da ake girmamawa a Afirka kuma wasu kafafen watsa labarai sun rawaito cewa ya gana da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kafin ya yi ƙira a cire wa waɗannan ƙasashe takunkumi.

Shugaban majalisar ECOWAS Omar Alieu Touray ya ce Janar Gowon ya gabatar da “saƙo mai girma”.

Touray ya tabbatar da cewa za a gudanar da taro na musamman na ƙugiyar ranar Asabar inda ya ƙara da cewa “shugabanninta za su yi nazari kan saƙonka yayin tattaunawarsu”.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like