Ɗaliban da suka zana jarabawar JAMB, su fara duba sakamakon daga yau talata – JAMB

1
269

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, ta bayyana cewa ɗaliban da suka zana jarrabawar JAMB na shekarar 2023, UTME, da su fara duban sakamakonsu daga yau Talata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar Dakta Fabian Benjamin ya rabawa manema labarai ranar Litinin a Legas.

A cewar Mista Benjamin, hukumar ta jinkirta sakin ne domin tabbatar da cewa an kammala duk wani binciken da ya dace, ba ya ga tabbatar da cewa an samu ma’ana da ma’auni, kafin sakin.

KU KUMA KARANTA: Hukumar JAMB ta sake ɗage jarabawar wasu ɗalibai a cibiyar Kaduna

“Yayinda ɗaliban ke tantance sakamakonsu a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, waɗanda suka zana jarrabawar amma suka fuskanci ƙalubale ba tare da sanin haka ba, ba za su ga sakamakonsu ba, sai dai su ga sanarwarsu na sake tsara musu wata jarabawar.

“Saboda haka, ana ƙira ga dukkan ɗaliban da suka zana jarrabawar da su duba sakamakonsu a ranar Alhamis, 8 ga watan Mayu ko kuma kafin ranar,” in ji shi.

Mista Benjamin ya buƙaci dukkan ɗaliban da ke ƙarƙashin waɗannan rukunonin da aka ambata, da su buga takardunsu a ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, zuwa Juma’a 5 ga watan Mayu, domin sanin lokaci da wurin da za a yi jarrabawar.

Ya kuma bayyana cewa ɗaliban su lura cewa za a haɗa su ne a wani wuri na tsakiya a cikin jihohinsu, domin zana jarrabawar saboda haka akwai buƙatar su buga takardar shedar zuwa ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu, domin yin isassun shirye-shirye. zauna jarrabawa.

1 COMMENT

Leave a Reply