Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya za su tsunduma yajin aiki

0
185

Jagorancin ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya, NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta tsunduma yajin aikin gama-gari a faɗin Najeriya daga ranar Talata 14, ga watan Nuwamban 2023.

Ƙungiyoyin sun cimma wannan matsaya ce a taron da suka gudanar yau Talata a Abuja bayan wata tattaunawa da suka gudanar.

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa tuni suka fara tuntuɓar mambobinsu a faɗin ƙasar domin shirya wa yajin aikin na makon gobe.

A tattaunawarsa da BBC, sakatareen tsare-tsare na ƙungiyar ƙwadagon, kwamared Nasir Kabir ya ce za su shiga yajin aikin ne kasancewar gwamnatin tarayyara Najeriya ba ta nuna aniyar cika alƙawurran da ta ɗaukar wa ƙungiyar ba.

A farkon watan Oktoba ne ƙungiyoyin ƙwadagon da gwamnatin Najeriya suka tattauna tare da samun matsaya domin kauce wa yajin aikin da ƙungiyoyin suka ƙuduri aniyar shiga a wancan lokaci.

KU KUMA KARANTA: ’Yan ƙwadago za su fara yajin aiki saboda kama shugabansu

Sai dai daga baya ƙungiyar NLC ta nuna rashin jin daɗin ta kan abin da ta ƙira rashin wani yunƙuri daga gwamnati na cika alƙawurran da ta ɗauka.

Haka nan kamun da ƴan sanda suka yi wa shugaban na NLC, Joe Ajaero a makon da ya gabata ya haifar da ƙarin rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.

Tuni dai NLC ta gabatar da wasu buƙatun da ta buƙaci a cika mata matuƙar ana son hana ta shiga yajin aikin da ta ayyana

Leave a Reply