Ƙungiyar NUJ reshen jihar Kano, ta naɗa sabbin shuwagabanni

0
56
Ƙungiyar NUJ reshen jihar Kano, ta naɗa sabbin shuwagabanni

 

Ƙungiyar NUJ reshen jihar Kano, ta naɗa sabbin shuwagabanni


Daga Idris Umar, Zariya

Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Kano, ta ƙaddamar da sabbin shuwagabannin ƙungiyarta na reshen jihar a hukumance da za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru 3 masu zuwa tare da buƙatar sabbin shugabannin ƙungiyar da su nuna ƙwarewa da kuma kare muradun ‘yan jarida a faɗin jihar.

Mataimakin Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Muhammad Tukur Umar ya buƙaci sabbin shugabannin da aka naɗa da su yi koyi da shugabannin da suka gabace su, inda ya jaddada muhimmancin yi wa al’umma hidima “Ya kamata ku inganta aikin ku tare da kare muradun mambobinku a duk inda suke,” in ji shi.

Shugaban mai barin gado, Abbas Ibrahim, ya yi tsokaci kan ƙalubalen da aka fuskanta a lokacin da ya fara jan ragamar ƙungiyar a shekarar 2018 yana mai cewa, “lokacin da muka zo hedikwatar ba ta cikin yanayi mai kyau, amma yanzu za a samu cigaba duba da yadda muka samu jagora nagari.”

Haka kuma ya ce ya amince da duk matsalolin da aka fuskanta musamman wajen samun bayanai, wanda ya bayyana a matsayin kayan aikinmu, sai ya yi ƙira ga ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu da su basu damar samun dukkanin bayanai idan buƙatar ta taso.

A ƙarƙashin jagorancin, Ibrahim, ƙungiyar ta samu nasarar warware duk wasu basussukan da ke maƙale ga ƙungiyar tare da barin asusun da Naira 819,597, inda ya nuna jin daɗinsa da samun damar yin aiki tare da yi wa sabbin shugabannin ƙungiyar fatan alheri.

KU KUMA KARANTA:NUJ jihar Yobe, ta nuna rashin jin daɗi da ƙara farashi da masu gidajen mai suka yi

Malam Suleiman Dederi, sabon shugaban ƙungiyar NUJ, reshen Jihar Kano ya sha alwashin kiyaye ɗa’ar aikin jarida tare da yin aiki da gaskiya, yana mai yin ƙudurin ci gaba da riƙe kyawawan halaye a aikin jarida.

Kwamared Kabiru Ado Minjibir Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta Najeriya ya ƙarfafawa gwamnatin jihar gwiwa wajen alakarta da ƴan jarida ganin irin rawar da suke takawa a cikin al’umma.

Bikin ƙaddamarwar wanda Abdulrzakak Bello Kaura da Sakataren ƙungiyar NUJ na shiyyar suka gabatar da rantsuwa ga sabbin shugabannin.
Waɗanda aka rantsar sun haɗa da Suleiman Dederi a matsayin Shugaba, sai Mustapha Gambo a matsayin mataimakin Shugaba, sai Abubakar Shehu Kwaru a matsayin Sakatare, sai Hauwwa Zahraddin a matsayin mataimakiyar Sakatare, da Nura Bala Ajingi a matsayin Ma’aji da kuma Abdullahi Hassan a matsayin Sakataren kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here