Ƙungiyar dattawan arewa ta yi ƙira ga Ecowas kan ta cire wa Nijar takunkumai

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar tuntuɓar juna ta dattawan arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum (ACF), ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta cire takunkuman da ta saka wa Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

A makon jiya ƙungiyar ta ACF ta soki batun aiki da ƙarfin soji da ƙungiyar Ecowas ɗin ta ce za ta yi idan sauran matakai sun gagara.

Dattawan sun kuma yaba wa ‘yan majalisar dokokin Najeriyar da suka yi watsi da maganar aiki da ƙarfin sojin kan jamhuriyar Nijar ɗin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *