Ƙasar Turkiyya ta jaddada aniyarta ta ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen Afirka

0
40
Ƙasar Turkiyya ta jaddada aniyarta ta ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen Afirka

Ƙasar Turkiyya ta jaddada aniyarta ta ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen Afirka

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada aniyar ƙasarsa ta ƙarfafa ƙawance da ƙasashen Afirka.

Ya jaddada hakan ne a taron bitar ministoci karo na uku na ƙawancen Turkiyya da Afirka a ƙasar Djibouti da ke gabashin Afirka a ranar Lahadi.

Ministan ya fara ne da isar da gaisuwar shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da yaba wa shugabannin Tarayyar Afirka bisa gudunmawar da suka bayar wajen taron.

Ya kuma yi magana kan adadin matasan da Afirka ke da su da albarkatu masu yawa, da kasuwanni masu tasowa, wadanda ya lura za su kai nahiyar “babban matsayi” a ƙarni na 21.

Duk da haka, ya kuma bayyana irin kalubalen da Afirka ke fuskanta, waɗanda suka hada da “ta’addanci, rashin daidaito, illolin sauyin yanayi, da rashin ci gaba da kuma yawaitar masu tafiya ci rani.”

Turkiyya, a matsayin abokiyar hulɗar Ƙungiyar Tarayyar Afirka tun daga shekarar 2008, ta yi kokarin raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ta hanyar da aka tsara da kuma nagartaccen tsari.

Fidan ya jaddada yadda Ankara ke sadaukarwa domin “samar da mafita ga matsalolin Afirka” yana mai tabbatar da matsayar Turkiyya da na ƙungiyar ta AU daidai da muradun 2063, na tabbatar da cewa an samu ci gaba mai kyau a faɗin nahiyar.

A yayin da yake magana kan matsalolin tsaro, Fidan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga ƙasashen Afirka wajen yaki da ta’addanci da samar da kwanciyar hankali a yankunan da tashe-tashen hankula suka shafa.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta la’anci kisan gilla da aka yi wa shugaban Hamas

Ya mai da hankali musamman kan halin da ake ciki a Sudan, inda ya bukaci ƙasashen duniya da su haɗa kai don ganin an tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma zaman lafiya mai ɗorewa.

Tun daga tsakiyar watan Afrilun 2023, sojojin Sudan da dakarun RSF suja soma wani ƙazamin yaƙi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu, a cewar MƊD.

Ƙasashen duniya da MƊD na ta jaddada kira kan a kawo ƙarshen tashe tashen hankula, yayin da rikicin ke barazanar jefa miliyoyin mutane cikin yunwa sakamakon karancin abinci a jihohi 13 cikin 18 na kasar Sudan.

Ta fuskar tattalin arziki, Fidan ya yi tsokaci kan yadda Turkiyya ta ƙara faɗaɗa kasuwanci da Afirka, wanda ya zarce dala biliyan 35 a shekarar 2023, kuma jarin da ta zuba ya kai kusan dala biliyan 7.

Ya jaddada cikakken tsarin ƙasarsa na bunƙasa dangantakar tattalin arziki da ci gaba, da ɓangaren kiwon lafiya da samar da abinci da kula da muhalli.

Har ila yau, ya jaddada cewa akwai ofisoshin jakadancin Turkiyya 44 a faɗin Afirka da kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen Afirka 38 a babban birnin Turkiyya.

A ƙarshe Fidan ya yi ƙira da a yi wa Majalisar Ɗinkin Duniya garambawul, musamman samar da daidaito ta ɓangaren wakilci a Kwamitin Tsaro.

Ya kuma yaba wa ƙasashen Afirka bisa goyon bayan da suke bai wa al’ummar Falasɗinu, sannan ya jaddada muhimmancin muryar Afirka a ƙungiyoyin duniya kamar G20.

Leave a Reply