Ƙasar Kamaru ta zamo ƙasar farko da ta fara sayen man Ɗangote daga ƙetare
Tan 60,000 na tataccen man fetur din da matatar ta fara fitarwa ketare zai isa ga kamfanin Neptune Oil, daya daga cikin manyan dillalan albarkatun man fetur a yankin tsakiyar Afirka.
Jamhuriyar Kamaru ta zama kasar ketare ta farko da ta sayi man fetur daga matatar Dangote.
Tan 60,000 na tataccen man fetur din da matatar ta fara fitarwa ketare zai isa ga kamfanin Neptune Oil, daya daga cikin manyan dillalan albarkatun man fetur a yankin tsakiyar Afirka.
KU KUMA KARANTA:INEC za ta baiwa ‘yan Najeriya mazauna ƙetare damar yin zaɓe daga ƙasashen da suke
Kamfanin ya bayyana cewa yana aiki tare da matatar domin kafa sahihin tsarin rarraba man da zai daidaita farashi da damammaki a ilahirin yankin.
Aliko Dangote na da shirin fitar da kaso 56 cikin 100 na man da yake tacewa zuwa ketare, duk da cewa wahalar samun danyen man na barazanar durkusar da ayyukan matatar tasa.
Matatar daka iya tace ganga 650, 000 a kowace rana ta fara sayar da fetur din da take tacewa a cikin Najeriya a watan Satumabn da ya gabata, inda kamfanin man Najeriya NNPCL ya kasance mai saye daya tilo.