Ɗan takarar kansila na AAC ya ka da na jam’iyya mai mulki PDP a Bauchi

0
112
Ɗan takarar kansila na AAC ya ka da na jam’iyya mai mulki PDP a Bauchi

Ɗan takarar kansila na AAC ya ka da na jam’iyya mai mulki PDP a Bauchi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar adawa ta AAC, Yunusa Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar Kansila a mazaɓar Papa a zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a jihar.

Da ya ke bayyana sakamakon zaɓen a ranar Asabar a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta Darazo, baturen zaɓen, Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce ɗan takarar jam’iyyar AAC ya samu ƙuri’u 1,156, inda ya doke abokin karawarsa na PDP, Ashiru Mohammed wanda ya samu ƙuri’u 1,053.

KU KUMA KARANTA:Abin da ya sa aka cire ni daga sarautar Mujaddadin Bauchi — Sanata Shehu Buba

Sai ɗan takarar jam’iyyar APC, Idris Mohammed da ya na uku da ƙuri’u 290.

“Ni Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayina na baturen zaɓe na mazabar Papa a zaɓen da ya gudana a ranar 17 ga watan Agusta na 2024. Cewa Yunusa Muhammad na AAC ya cika ƙa’idar da doka ta tanada nake ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe”, inji shi.

Leave a Reply