Ƙungiyoyin ƙwadago sun sanar da janye yajin aikinsu

0
180

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya na NLC da TUC sun sanar da janye yajin aikin da suka fara ranar Talata.

Ƙungiyoyin de sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani ne ranar Talatar domin nuna ɓacin ransu da dukan da aka yi wa shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero a jihar Imo a kwanakin baya.

A lokacin dai Ajaero ya jagoranci ma’aikatan Imo domin wata zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan wasu manufofin gwamnan jihar, Hope Uzodinma.

Sai dai daga bisani wasu ’yan daba da ake zargin magoya bayan Gwamnan ne suka lakaɗa masa duka sannan ’yan sanda suka tsare shi.

Hakan dai ya janyo fushin ƙungiyoyin ƙwadagon, waɗanda suka tsunduma yajin aiki a ranar talata don nuna goyon bayansu gare shi.

KU KUMA KARANTA: Ba don kishin ƙasa ‘yan ƙwadago suka tsunduma yajin aiki ba – Gwamnati

Aminiya ya rawaito cewa Mashawarcin Shugaban ƙasa kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sa labule da ƙungiyoyin a ranar Laraba, a kan yajin aikin, inda ya ce tuni ma aka kama mutum biyu da ake zargi da duka Ajaeron.

Wakilinmu ya jiyo daga wasu jiga-jigan ’yan ƙwadago yayin taronsu na musamman suna cewa sun amince da ɗaukar matakin ne bayan nazarin dukkan alkawuran da Ribadun ya yi musu.

Shi ma Sakataren ƙungiyar ma’aikatan gwamnati ta AUPCTRE), Kwamared Sikiru Waheed, shi ma ya tabbatar da labarin ga ’yan jarida.

Leave a Reply