Ƙasar Rasha ta nesanta kanta daga masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar Najeriya

0
64
Ƙasar Rasha ta nesanta kanta da masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar Najeriya

Ƙasar Rasha ta nesanta kanta daga masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar Najeriya

Ƙasar Rasha ta nesanta kanta daga duk wasu masu ɗaga tutocin ƙasarta a zanga-zangar da ake yi a Najeriya kan tsadar rayuwa.

Tun bayan fara zanga-zangar ranar 1 ga watan Agustan nan ne aka dinga ganin gungun mutane a jihohi da dama a fadin ƙasar suna ɗaga tutar ƙasar Rasha a yayin tattakin.

Masu sharhi kan harkokin yau da kullum sun yi ta jan hankalin ‘yan Najeriya a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta cewa hakan illa ne ga dimokuraɗiyyar ƙasa mai cikakken ‘yanci irin Najeriya wadda take ƙarƙashin mulkin siyasa.

A sanarwar da ya fitar a jiya Litinin, Ofishin Jakadancin Rasha da ke Najeriya ya ce “mun lura da rahotannin da kafafen watsa labaran Najeriya ke fitarwa da kuma yaɗuwar wasu hotuna da bidiyoyi a intanet da ke nuna masu zanga-zanga a arewacin ƙsar suna ɗaga tutocin Rasha suna ƙiran sunan Shugaba Vladimir Putin.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: BUK ta dakatar da koyarwa zuwa wani lokaci

“Gwamnatin Tarayyar Rasha da kuma wasu jami’an Rasha ba su da hannu a cikin waɗannan ayyukan ta kowace hanya. Kamar kullum, muna jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashen waje ciki har da Najeriya,” in ji sanarwar.

Rasha ta ƙara da cewa “wannan aniyar ta masu zanga-zangar ta ɗaga tutocin Rasha zaɓi ne na ɗaiɗaikun mutane, kuma ba sa nuna wani matsayi ko manufofin gwamnatin Rasha kan batun.

“Muna mutunta dimokuraɗiyyar Najeriya kuma mun yi imanin cewa zanga-zangar lumana bisa ga dokar Najeriya alama ce ta dimokraɗiyya.

Duk da haka, idan waɗannan abubuwan sun haifar da duk wani rikici ko tashin hankali za mu yi Allah wadai da su.”

Leave a Reply