Ƙasar Sri Lanka ta zaɓi sabon shugaban ƙasa

0
561

Kasar Sri Lanka ta zabi sabon shugaban kasa, to amma me zai faru da tsohon shugaban ƙasar, Gotabaya Rajapaksa?

Shugaba Rajapaksa ya tsere daga ƙasarsa ta haihuwa zuwa Maldives a ranar 13 ga watan Yuli sannan daga baya ya hau jirgi zuwa Singapore, kuma daga can ne ya sanar da murabus dinsa.

Sai dai ba a san ko zai ci gaba da zama a can ba.

KU KUMA KARANTA: Sri Lanka: Masu zanga-zanga sun mamaye fada har sai shugabanni sun sauka

Ministan harkokin wajen Singapore ya ce Rajapaksa ya shiga ƙasar a wata ziyara ta dan wucin-gadi, amma wani jami’i a gwamnatin Sri Lanka ya ce zai koma kasar nan gaba.

Sai dai wata ƙungiyar kare haƙkin jama’a ta shigar da korafin kan tsohon shugaban ƙasar a ofishin babban attoni janar na ƙasar kan aikata laifin ta’addanci, inda take son a kama shi saboda rawar da ya taka a yaƙin basasar Sri Lanka.

Wasu rahotanni sun nuna cewa zai iya tafiya Saudiyya ko Hadaddiyar Daular Larabawa.

Leave a Reply