Zaɓen 2023: An tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC

3
572

Gwamnatin Najeriya ta ɗauki ƙwararan matakan tsaro a ofisoshin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ke faɗin ƙasar.

Gwamnatin ta tura jami’an tsaro na DSS da sojoji da jami’an hukumar kashe gobara ofisoshin hukumar ta INEC domin tsaurara tsaro gabannin zaɓen 2023.

Ta kuma umarci jami’an su inganta tattara bayanan sirri domin daƙile duk wani yunƙuri na rikici ko ɓata gari a makonni masu zuwa gaba.

Babban Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba ne ya shaida hakan bayan tattaunawa da shugabanni jam’iyyun siyasa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.

Ya ce a cikin mako shida, an samu rigingimu aƙalla 52 a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da Ogun da Osun.

Akwai kuma harin da aka kai wa magoya-baya a gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi irinsu Borno da Kaduna da Zamfara da dai sauransu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana tsare da wasu da ake zargi na da hannu a waɗannan rikice-rikice, kuma za a gurfanar da su domin fuskantar hukunci.

3 COMMENTS

Leave a Reply