Daga Fatima GIMBA, Abuja
millar mutum 164 ne suka rasu a Najeriya sakamakon cutar zazzaɓin Lassa tun daga watan Janairun 2022 zuwa yanzu.
Cikin rahoton da ta saba wallafawa kan halin da ake ciki, hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ce an tabbatar da mutum 857 da suka kamu da cutar zuwa yanzu a faɗin ƙasar.
Mutanen da suka kamu sun fito ne daga jiha 29, ko kuma ƙaramar hukuma 99, a cewar NCDC. Kazalika, ma’aikatan lafiya 54 ne suka kamu da cutar.
“Lissafi ya nuna cewa Jihar Ondo na da kashi 30 cikin 100 na mutanen da suka kamu, Edo na da 26, Bauchi kuma na da 14,” in ji rahoton.
“Cikin sati na 29, adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya haura zuwa 10 daga mutum biyar da aka samu a sati na 28. An same su ne daga jihohin Edo da Ondo.
“Jimilla daga sati na 1 zuwa na 29 a 2022, an samu mutuwar mutum 164.”