Zan Tabbatar Da Kwararru Ke Kula Da Al’amura Ba Kamar Sanya Dan Jarida A Sahen Tsaro Ba – Shehu Sani

0
324

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon Sanatan Shiyyar Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya bayyana cewa idan ya zama Gwamnan Kaduna, zai tabbatar da sanya Kwararru su kula da al’amura a duk sashen da suka dace wanda hakan zai tabbatar da samun inganci al’amura.

Sanata Shehu Sani, wanda ya kai ziyara cibiyar Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya, (NUJ), reshen Jihar Kaduna, a yau ranar talata, ya bayyana hakan ne yayin wani zaman ganawarsa da manema labarai na musamman, inda ya furta cewa Jihar Kaduna na cikin wani mawuyacin hali da ke bukatar agaji da taimako na gaugawa domin ceton Jihar da al’ummar Jihar.

Ya kara da cewa, daga cikin kudirorinsa shida da yake dasu a kan Jihar idan Allah Ya kai shi ga cin wannan nasarar zama Gwamnan, matsalar rashin tsaro na daga cikin abubuwan da zai tabbatar da kawarwa dasu ta hanyar yin aiki da Kwararru, kana da samarwa Jami’an tsaro kayan aiki masu inganci, ba kamar yadda a yanzu aka dauko Dan Jarida aka ba shi rekon sashen al’amuran tsaro ba.

Ya ci gaba da cewa al’ummar Jihar Kaduna sun ga banbancin dake tsakanin mulkin daya gabata da wanda ake ciki a yanzu, don haka ya kamata al’umma su yi karatun ta natsu muddun har ba so suke su ci gaba da zama a mawuyacin halin kunci, bakar azaba da wahalar da ake fuskanta a mulkin ta APC ba.

Ya ce “asalina dan APC ne domin mu muka Kafa ta kuma nasan duk abin da ta ke kunshe da ita a cikin Jihar, kuma ni lokacin da naci takara babu wanda ya tsaya mun domin ba ni da uban gida, sai Ubangijina dana dogara da shi, saboda haka har yanzu ina nan a matsayin da nake na yin fafutukata da Gwagwarmaya yadda na saba ba tare da wani uban gida ba kuma na dogara da Ubangijina.”

“Na farko a kudirorina shi ne hada kan al’ummar Jihar ta yadda za a samu zaman lafiya, na biyu yaki da kalubalen matsalar rashin tsaro wanda ya tayarwa da al’umma hankali, domin a yanzu duk jokarin da ake na yaki da ta’addanci a Jihar, karamar hukuma Kaduna ta Arewa da ta kudu ne kawai al’amuran ke yin tasiri banda sauran kauyukan.”

“Na uku, zan tabbatar da samar da Kayan more rayuwa da raya ciki da wajen Jihar tare da samar da tsaro, ba kamar yadda muke gani a yanzu an saka fitilun kan hanya ba amma Jama’a na rayuwa cikin tsoro ba. Na hudu zan raya sashen wasannin motsa jiki da abubuwa daban-daban, kana na biyar zan Farfado da bangaren Noma wanda a yanzu manoman Jihar ke tsoron zuwa goma, domin tsarina ba irin nasu bane.”

Acewar Kwamared Shehu Sani, ga duk wanda yasan shi, yasan cewa shi mutum ne mai cika alkawari da dattaku wanda idan ya furta zai yi abu, to babu makuwa zai aikata, kana mutum ne da yasan Yanci da hakkin Dan-Adam, don haka ba ya tamtama a kan duk wasu kudirorinnsa idan Allah Ya kai shi ga zama Gwamnan Jihar bayan lashe Zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta PDP.

Hakazalika, Dan takarar Gwamnan, ya bada tabbacin cewa zai yi mubayi’a ga duk wanda samu nasarar lashe Zaben fidda gwanin, amma ya shawarci duk wakilan Jam’iyyar masu zaben yan takarar da Kada su bari a rude su da wasu yan Kudi da nan gaba za su yi danasanin aikata wannan kuskuren na zaben wanda bai zai iya yin nasara ba a zaben duka gari, domin shi kadai ne yan Jam’iyyar adawa ke shakkar tsayawarsa a matsayin dan takarar Jam’iyyar PDP.

A karshe, Sanata Shehu Sani, ya taya sabon shugabancin Kungiyar ta (NUJ) Kaduna wanda ke karkashin Jagorancin Hajiya Asma’u Yawo Halilu Murnar yin nasarar, kana ya yi musu fatan alheri na Allah Ya basu ikon sauke nauyin da ke kansu dukda kasancewar mace ce Jagorar reshen Kungiyar a karon farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here