Zaben 2023: Kwamishinoni Da Masu Bada Shawara Sun Fara Ajiye Mukaman Su A Kano

0
410

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SAKAMAKON sharudda da kuma ka’idoji da sabuwar dokar zabe ta 84 (12) da kuma umarnin da Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar cewa wadanda aka nada kan mukaman siyasa masu bukatar yin takara su sauka zuwa yau litinin, wasu kwamishinoni sun fara sauka daga mukaman su domin shirin shiga fagen zabe gadan-gadan.

Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Ganduje ya bada umarni ga dukkanin masu sha’awar shiga fagen zabe a 2023 su ajiye mukaman su zuwa ranar litinin 18-4-2022, wanda kuma hakan ta sanya ya zuwa aiko da wannan labari, kwamishinoni 7 da wasu masu baiwa Gwamna Shawara sun gabatar da takardar su ta ajiye aiki domin tsunduma cikin harkokin zabe sosai.

Cikin kwamishinonin da suka ajiye aiki akwai kwamishinan kananan hukumomi Murtala Garo da na raya karkara Musa Iliyasu Kwankwaso, sai Muktar Ishaq Yakasai kwamishinan aiyuka na musamman, da Nura Dankadai kasafin kudi, Sadiq Wali na ma’aikatar ruwa da Mahmoud Muhammad ma’aikatar ciniki da kuma mataimakin Gwamnan Jihar kano Nasiru Gawuna wanda ya ajiye mukaminsa na kwamishinan ma’aikatar gona.

Haka kuma yanzu haka akwai masu baiwa Gwamna Shawara wadanda suka fara ajiye mukaman su domin shiga fagen yakin neman zabe domin bin umarni da kuma dokar zaben da aka yiwa gyara domin kara tsaftace dimokuradiyya, wanda kuma a binciken da wakilin mu ya gudanar, kafin cikar wa’adin umarnin ajiye mukamai akwai sauran mutanen da zasu sauka daga mukaman su a Jihar ta Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here