Zaɓen 2023: Wa’adin Kwanaki 111 INEC Ta Bai Wa Jam’iyyu Su Mika Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

0
658

Daga; Rabo Haladu.

HUKUMAR zabe ta Kasar Najeriya, (INEC), ta umarci Jam’iyyun kasar su mika mata sunayen ‘Yan takararsu na shugaban ƙasa daga yanzu zuwa 17 ga watan Yunin 2022.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake sanar da jadawalin zaben 2023 a taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar a Abuja.

Hakan na nufin dole APC da PDP da ma sauran jam’iyyu da za su fafata a zaben 2023 su aika sunayen masu tsaya musu takarar shugaban kasa nan da kwana 111 masu zuwa.

Ya ce za a “mika fom na tsayawa takarar shugaban kasa da majalisun dokokin tarayya ga INEC ta yanar gizo daga tara na safen Juma’a 10 ga wata zuwa 17 ga watan Yuni na 2022.”

Daya daga cikin ɓangarorin jadawalin zaɓen masu muhimmanci shi ne; sanarwar zaɓe wadda ya kamata a yi ƙasa da kwanaki 360 kafin lokacin kaɗa ƙuri’a ba za ta yiwu ba game da zaɓen 2023 saboda lokaci ya ƙure.

Wannan dalilin ne ya sa hukumar zabe ta sauya ranakun zaben shugaban ƙasa daga 18 na watan Fabarairu da kuma na gwamnoni mako biyu bayan haka kamar yadda ta tsara tun farko, domin ta tabbatar ta yi biyayya ga tanade-tanaden sabuwar dokar zabe.

Game da haka, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin tarayya a ranar Asabar 25 ga watan Fabarairu na shekarar 2023, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi mako biyu bayan haka a ranar Asabar 11 ga watan Maris

Sauran tsare-tsaren ranakun da suka shafi baban zabe sun hada da

28 ga Fabarairu 2022: Wallafa ranakun gudanar da zaɓe. 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin 2022: Gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu da kammala sauraron ƙorafe-ƙorafe. 1 zuwa 15 ga Yulin 2022: Aika sunayen ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar Jiha ga INEC ta shafinta na intanet. 28 ga Satumban 2022: Fara yawon kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya.

12 ga Oktoban 2022: Fara kamfe na ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha. 23 ga Fabarairun 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya. 9 ga Maris na 2023: Kammala kamfe na ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha.

Shugaban INEC Farfesa Yakubu ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.

A cewarsa, za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023.

Shugaban INEC ya ce an zaɓi ranakun ne saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here