‘Yar shekara 13 mai matsalar Aljanu da ta ɓace a Kaduna, an gano ta a Maiduguri

0
401

Wata yarinya ‘yar shekara 13 da ta ɓace makonni biyu da suka gabata a Kaduna, amma an samo ta a jihar Borno, ta sake haɗuwa da ‘yan uwanta.

An gano yarinyar tana yawo a tashar Borno Express Corporation da ke Maiduguri inda aka miƙa ta ga ‘yan sanda.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ‘yan sandan sun gudanar da bincike na gaskiya domin gano dangin yarinyar.

ASP Kamilu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Maiduguri yayin da yake miƙa yarinyar ga mahaifinta, ya ce babban jami’in tsaro na tashar, Ahmadu Buba ne ya kawo ta ga ‘yan sanda.

“Ta kasance a ƙarƙashin kulawar DPO na ofishin ‘yan sanda na cikin garin Maiduguri, CSP Hadiza Musa Sani, inda aka fara kai rahoton lamarin kimanin makonni biyu da suka wuce.

“Bayan bincike mai zurfi, mun gano inda iyayenta suke a Kaduna waɗanda yanzu haka suke nan domin karɓar ta a hukumance.”

Mahaifin yarinyar Ado Usman, ya ce yarinyar da ke da “matsalar aljanu”, ta yi ɓatan dabo sau da yawa a baya. “Wannan ba shi ne karon farko ba, akwai lokacin da ta hau babur mai ƙafa uku aka same ta a kusa da Kano.

KU KUMA KARANTA:An samu budurwar data ɓata daga Legas, a jihar Bauchi

“Ta kasance tana tashi a firgice a cikin dare tana cewa wani yana kiranta ta biyo shi a wani wuri; muna iyakar ƙoƙarinmu kuma za mu ci gaba da yi mata addu’a,” in ji Mista Usman.

Mahaifin yarinyar yabawa ‘yan sanda da duk waɗanda suka taimaka wajen gano ta da kuma tabbatar da tsaron yarinyar.

Yarinyar ta kasance taki ta amsa lokacin da aka tambaye ta ta bayyana yadda ta yi tafiya daga Kaduna zuwa Maiduguri.

Leave a Reply