Connect with us

Gasa

‘Yar shekara 10 ta lashe gasar haɗa baƙi ta ‘Spelling Bee’ a Borno

Published

on

Wata yarinya ‘yar shekara 10 mai suna Aisha Modu-Mustapha daga makarantar firamare ta Sanda Kyarimi ta lashe gasar haɗa baƙin boko ta ‘Spelling Bee’ ta shekara-shekara da gidauniyar Inara ke gabatarwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Matashiyar Aisha ta rubuta kalmomin Whirligig, Quarreling, Administration, Willingly, Spaceless, Peasant da sauran su, har ta doke abokan hamayyarta Muhammad Muhammad-Dawule, daga makarantar Gamboru Primary School, da Bukar Muhammad daga makarantar Ibrahim Damchida.

Gidauniyar ta bai wa waɗanda suka yi nasara a gasar kwamfyutocin tafi-da-gidanka, kyautar tsabar kuɗi da kuma kayan karatu na maƙudan kuɗi.

Da take jawabi bayan kammala gasar a ranar Alhamis, wacce ta kafa gidauniyar Aisha Waziri-Umar, ta ce an shirya gasar ne domin tallafawa da kawo sauyi ga ilimi a jihar Borno.

Mai ba da agajin ta ƙara da cewa alfanun da ake samu ya wuce ƙwarewa a harshe hakan na taimaka wa yara wajen samun ƙwarin gwiwa da fahimtar juna da fahimtar jama’a, da kuma samun nutsuwar yin abinda duk ake buƙata a yanayi na matsin lamba.

Shima, da yake nasa jawabin Manajan shirin na gidauniyar Inara, Usman Umar-Dagona, ya bayyana cewa gidauniyar wata ƙungiya ce mai zaman kanta, wacce take tallafawa ilimi, ƙirkire-ƙirkire da kuma marasa galihu a Najeriya, musamman a Arewa maso Gabas ta hanyoyi daban-daban na ayyukan al’umma.

A kwanakin baya ne gidauniyar ta ƙaddamar da cibiyarta ta farko ta Codeing, Robotics da kuma Programming a yankin Arewa maso Gabas a Maiduguri, inda aka horas da matasa 30 sana’o’i daban-daban na fasahar zamani da suka haɗarda fasahar ƙira mutum-mutumi da codeing.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: ‘Yar shekara 10 ta lashe gasar haɗa Baƙi ta ‘Spelling Bee’ a Borno - LEGEND FM DAURA

  2. Pingback: ‘Yar Kaduna ta lashe gasar lissafi ta ƙasa da ƙasa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Gasa

Babu rashin jituwa tsakanina da Salah – Klopp

Published

on

A makon da ya gabata ne Salah da Klopp suka yi musayar kalamai a gaban jama’a a wasan da Liverpool ta buga da West Ham wanda aka tashi da ci 2-2.

Kocin Liverpool Jurgen Klop ya dage da cewa babu wata ’yar tsama tsakaninsa da Mohamed Salah saboda an riga an sasanta lamarin.

Klopp ya ce tsawon lokacin da suka kwashe suna mu’amulla da ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya sa dangantakarsu ba ta shafu ba duk da ‘yar tangarɗar da aka samu.

KU KUMA KARANTA:Ronaldo ya ce yana sa ran cin ƙarin ƙwallaye a 2023

A makon da ya gabata Salah da Klopp suka yi musayar kalamai a gaban jama’a a wasan da Liverpool ta buga da West Ham wanda aka tashi da ci 2-2.

Bayan an kammala wasan, da aka tambayi Salah me ya faru, sai aka ji yana cewa, “ idan na yi magana za a yi tashin hankali yau.”

Klopp dai ya ce batun “ba wani abu ba ne” kuma “babu wata damuwa” a tsakaninsu.

Continue Reading

Addini

Kano da Bauchi sun lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa ta 2023

Published

on

Malama Zainab Aliyu Muhammad daga jihar Kano ta zama gwarzuwar gasar Alƙur’ani ta ƙssa ta shekarar 2023 a ɓangaren mata a hadda da tafsiri.

A ɓangaren maza kuwa, Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir daga Jihar Bauchi ne ya zama gwarzon shekara a musabaƙar karo na 38, wadda aka kammala a Jihar Yobe.

Mai Masaukin Baki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karamma Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano da kyautar mota ƙirar Honda Accord.

Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir kuma gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar mota ƙirar Honda Accord.

Sannan ya ba da kyautar bas mai ɗaukar mutum 18 ƙirar Toyota Hummer ga Kwamitin shiryar musabaƙa na ƙasa don ci gaba da ɗawainiyar gasar Alƙu’rani.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka fara gasar Alƙur’ani ta ƙasa karo na 38 a Yobe

A ranar Asabar ɗin nan aka kammala gasar karatun Alƙur’anin ta ƙasa karo na 38 a Damaturu, fadar Jihar Yobe inda alarammomi daga sassan Najeriya suka nuna bajintarsu.

A lokacin rufe gasar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa matasan da suka shiga wannan gasar ta Karatun Alƙur’ani Mai Girma rukuni-rukuni, sannan ya yi musu fatan alheri.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da gasar a Yobe cikin kwanciyar hankali kuma a bisa tsari ba tare da an samu cikas ba.

Shi ma Shugaban Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya ɗauki nauyin gasar da kuma yadda aka gudanar da ita cikin nasara.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Danfodiyo ne dai ke shirya Gasar Alƙur’ani ta Ƙasa a Najeriya, kuma wanan shi ne karo na 38.

Mahalarta bikin rufe gasar ta Alƙur’ani sun haɗa da Gwamna Jihar Gombe, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamna Jihar Borno, Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba.

Sai masu girma sarakunan Jihar Yobe gaba ɗaya, ƙarƙashin Mai Martaba Sarkin Fika, sai Mai Martaba Shehun Dikwa da ya wakilci Mai girma Shehun Borno, sai Mai girma Sarkin Bauchi da sauran manya-manyan baƙi.

Continue Reading

Gasa

Za a gudanar da gasar tseren raƙuma mafi girma a Saudiyya

Published

on

Hukumar da ke shirya gasar tseren raƙuma ta Saudiyya ta ce gasar tseren raƙuma da za a gudanar a wannan shakera a ƙasar za ta kasance mafi girma da aka taɓa yi a tarihin ƙasar.

Hukumar ta fitar da jadawalin gasar da ta ce za a kwashe kwanaki 38 ana gudanarwa.

Jadawalin gasar ya nuna cewa za a fara gasar wadda kusan mutum 600 za su fafata, cikin tsakiyar watan Agusta.

KU KUMA KARANTA: Rundunar Sojojin Najeriya na gudanar da gasar motsa jiki tsakanin sojojin ƙasar

Gasar wadda za a gudanar a birnin Taif ƙarƙashin jagorancin Yarima mai jiran gadon sarautar ƙasar Mohammed bin Salma, an shirya ta ne da nufin nuna muhimmanci da martabar raƙuma a al’adun ƙasar.

An tsara gudanar da gasar ne mataki-mataki, inda za a fara matakin farko na gasar a garin Tabuka, sannan a ƙarƙare gasar a birninTaif.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like