Yar najeriya ta mutu ana tsaka da ƙara mata girman mazaunai a Indiya

0
446

Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 28 ta sheka lahira yayin da ta bazama kasar Indiya don a kara mata girman mazaunanta, LIB ta ruwaito.

Marigayiyar

Amelia Pounds ta tattara dukiyarta inda tace ba za ta zauna tana ganin mata na juyi yayin da ita kuma ta ke zaune ba, hakan yasa ta lallaɓa don likita ya kawo mata mafita.

An tattaro bayanai akan yadda ‘yar kasuwar ta rasa rayuwarta ana tsaka da aikin a wani asibiti wanda aka sakaya sunansa a cikin New Delhi, ranar Juma’a da safiyar 7 ga watan oktoban 2022.

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, Vera Sidika ta tabbatar da aukuwar lamarin ta shafinta.

Leave a Reply