‘Yar Gombe mai shekaru 14 ta kafa tarihi a fannin lissafi

1
338

Yarinyar, yar jihar Gombe mai shekaru 14 ta kafa tarihi bayan ta sami lambar yabo ta ƙasar waje har guda 7 a fannin lissafi.

kwararriyar ilimin lissafi, Fatima Adamu Maiƙusa, daga jihar Gombe, ta lashe lambobin yabo na lissafi har guda bakwai.

Fatima na karatu ne a makarantar Nigerian Turkish International (NTIC) da ke jihar Kano.

Ta samu lambobin yabo na ƙasa da ƙasa guda bakwai a fannin lissafi a faɗin duniya da suka haɗa da gasar Lissafi ta Amurka (AMC 08), da gasar Ilmi ta Duniya a Jakarta babban birnin Indonesiya, sai gasar ƙalubalen Lissafi na Duniya a birnin Bangkok na ƙasar Thailand, da sai gasar lissafi ga Kangourou Sans Frontiers (KSF) da kuma gasar lissafi ta Future Intelligence Students Olympiad (FISO), sai gasar lissafi babu iyaka a kasar Bulgaria, da gasar lissafi ta Komodo a kasar Indonesia.

1 COMMENT

Leave a Reply