’Yansanda a Borno sun kama ɓarayi 2 da ƙwato wayoyi 25

0
28
’Yan sanda a Borno sun kama ɓarayi 2 da ƙwato wayoyi 25

’Yansanda a Borno sun kama ɓarayi 2 da ƙwato wayoyi 25

Rundunar ’yansandan Jihar Borno, ta kama mutum biyu da ake zargin masu ƙwacen wayar salula ne a Maiduguri.

Rundunar ta kuma ƙwato wayoyi 25 da ake zargin na sata ne a hannunsu.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Yusufu Mohammed Lawal, ne ya tsara aikin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

Ya ce matakin na daga cikin ƙudirin rundunar na tabbatar da tsaron al’ummar jihar.

ASP Daso, ya ce rundunar Kai Ɗaukin Gaggawa (RRS) ce, ta kama mutanen biyu, Ibrahim Abubako da Ibrahim Mohammed, a lokacin da suke kan hanyar Damboa a cikin garin Maiduguri.

A cewarsa, “An same su da wayoyi 25, kuma bayan tambayoyi, sun amsa cewa sun ƙwace wayoyin daga hannun jama’a a ƙauyukan Tashan Alade, Miringa, Kwaya Kusar da Biu da ke kan iyakar Jihohin Borno da Adamawa.”

KU KUMA KARANTA: Yansanda a Kano sun kama mutane 2 kan zargin zuba ruwan rubutu a Rijiya

ASP Daso, ya ƙara da cewa: “Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma ana shirin gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.

“A yanzu haka, rundunar tana ƙoƙarin mayar wa mutanen da suka ƙwato wayoyin a hannunsu.”

Rundunar ta kuma yi ƙira ga jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abun zargi, musamman yayin da ake shirin bukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Ta kuma tabbatar da aniyar ci gaba da kare lafiyar al’ummar jihar.

Leave a Reply