‘Yan sanda sun kama wani da ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
An kama wani mutum kan laifin sanya almakashi da cokali a cikin al’aurar wata yarinya ’yar shekara takwas a Jihar Jigawa.
Mutumin mai shekaru 32 ya yi wa yarinyar mummunan rauni a gabanta har sai da ta sume, a sakamakon wannan aika-aika da ya yi mata.
Kakakin ’yan sanda na jihar, DSP Lawan Shi’isu Adam, ya ce jami’an tsaro sun kama mutumin ne bayan da ya yaudari yarinyar zuwa banɗaki a wani kamfanin sarrafa ruwan leda a garin Dutse, inda ya yi mata wannan ɗanyen aiki.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu
Jami’in ya bayyana cewa mutumin ya sha cin zarafin yarinyar, kuma yana yi mata barazanar kashe ta da iyayenta, idan har ta kuskura ta sanar da wani.
DSP Lawal ya ce a halin yanzu mutumin yana tsare a hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka an ’Yan Sanda (SCID) da ke jihar.