‘Yan sanda sun ceto ɓarawon waya

Daga Maryam SULAIMAN, Abuja

Rundunar ‘yan sandan sintiri ta RRS a Legas ta ceto Chinedu Ike, mai shekaru 25, daga ‘Yan daukar doka a hannu, a watan Satumba, 2022 a Iyana Oworo, bayan da ya saci wayar hannu.

Wasu fusatattun mutane ne suka yi masa dukan tsiya kafin daga bisani rundunar ta kai shi asibiti. An sallame shi bayan wasu kwanaki.

Wanda ake zargin ya bi salon da ya saba, ya shiga wata mota da aka faka, domin ya sace wayar direban a Iyana Oworo.

Jami’an RRS ne suka kama shi a lokacin da wadanda suka san Chinedu, suka jawo hankalin direban ya duba wayarsa.

Jami’an mu sun kwato wayar Infinix Note 10 ta direban daga jakar Chinedu.

An kuma kai shi kotu inda aka yanke masa hukunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *