Yan sanda sun ƙaddamar da manhajar daƙile satar mota a Najeriya

0
479

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya yi nasarar kammalawa tare da kaddamar da babbar cibiyar rajistar motoci ta CMR da ke hedikwatar rundunar da ke Abuja wadda ke da zama a sashen yada labarai da fasahar sadarwa.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya aike wa Neptune Prime, ya ce ci gaban da aka samu ya yi daidai da kokarin Sufeto-Janar na tabbatar da yanayin da ake amfani da shi na zamani don gudanar da aikin ‘yan sanda a ƙasar don ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakan da suka dace wajen rigakafin laifuka, bincike da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

Ya ce sabuwar cibiyar rajistar motoci ta tsakiya da aka samar, za ta bai wa jama’a damar bayar da rahoton motocin da aka sace tun daga ranar 1 ga watan Janairu, 2018, da har yanzu ba a kwato su ba, don shigar da bayanan motar a dandalin yanar gizo, don yiwuwar dawo da su ga masu shi.

Dandalin zai kuma aiwatar da bayanan motocin don tallafawa ayyukan ‘yan sanda da ƙokarin inganta tsaron kasa.

“Nazarin na’urar ta CMR ta cika da cibiyoyin umarni guda 2 a Abuja da Legas, cibiyoyin watsa labarai na CMR 37 a fadin ƙasar nan da kuma babban birnin tarayya, inda motocin sintiri na guda 200 da za suyi aikin tabbatar da shirin, tare da tantance lambbobin kowace mota a matsayin wani bangare na rukunin na farko”. In ji shi.

Adejobi ya ƙara da cewa, Sufeto-Janar na ‘yan sandan yayi kira ga ‘yan Nijeriya da sauran mazauna ƙasar nan da su yi amfani da manhajar ya https://reportcmr.npf.gov.ng don sanya bayanan motar su a yanar gizon daga ranar Laraba. 7 ga Disamba, 2022, a matsayin matakin tsaro na hana sata da sake yin rajista.

Leave a Reply