‘Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun jikkata wasu da dama

0
11
'Yan bindiga sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu da dama

‘Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun jikkata wasu da dama

Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun harbe mutum tara har lahira tare da jikkata wasu da dama a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Da misalin ƙarfe 8 na dare ne maharan suka kai farmaki suna harbi kan mai uwa da wabi a yankin Tattara ranar Asabar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “bagatatan suka far mana a cikin dare, mutum tara sun rasu wasu biyu na kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai baya ga wasu da suka raunuka da dama.”

Kimanin shekara guda ke nan da aka kai makamancin harin tare da ƙona gidaje a yankin na Tattara.

Leave a Reply