Connect with us

Noma

‘Yan bindiga sun datse wa manomi hannayensa a Zamfara

Published

on

Wani manomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, mai suna Malam Sama’ila Muhammad, wanda ƴan bindiga suka datse wa hannayensa biyu ya ce ya miƙa lamarinsa ga Allah kuma shi ne kaɗai zai saka masa.

Manomin da ke zaune a ƙauyen Walu a ƙaramar hukumar Kauran Namoda ya bayyana cewa shi da ƴan uwansa sun ci karo da ƴan bindigan ne bayan sun fatattaki wasu ɓarayi da suka je satar kaji a gidansu kusan sha biyun dare, fiye da mako guda da ya wuce.

Malam Sama’ila ya shaida wa BBC cewa “bayin Allah ne suka shiga gidanmu, suka kama kaji sai suka fita, sai na ji sun shiga wajen ƙanina suna bugunsa, sai na ce jama’a kun ji suna bugun auta, ku taho mu je gare su,”

“Ashe sun ji, sai suka tsallaka katanga suka fita da gudu, sai muka bi su, da muka bi su sun yi nisa sai nake cewa ƙannena su dawo tun da sun tafi su dawo, ashe waɗannan masu bindiga sun koro bisashe (dabbobi).”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Bagudu ya halacci taron bunƙasa harkar noma a Abuja

Published

on

Daga Idris Umar, Zariya

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi na ƙasa a ranar Talata 16/04/2024, Ya halarci wani shiri na musamman a babban birnin tarayya Abuja domin bunƙasa sha’anin harkokin ayukkan gona a faɗin Najeriya.

Shirin wanda yake ƙarƙashin gwamnatin ƙasar Jamus (Germany ) da kuma ƙungiyar GIZ zai bayar da gagarumar gudumuwa wajen bunƙasa sha’anin ayukkan gona a Najeriya.

Bagudu ya bayyana alfanun da ke akwai ta haɗaka da ƙungiyoyi ire-irensu GIZ ta hanyar musayar ilmi da amfani da zamani wajen cimma manufa, Bagudu ya ƙarfafawa mutanen da suka halarci shirin da su rinƙa shirya taron ƙara wa juna sani domin cimma kyakkyawar manufar ciyar da ƙasa gaba.

KU KUMA KARANTA: Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Bagudu ya ƙara fayyace cewar haɗaka na da matuƙar muhimmanci domin ta hakan ne za’a samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi da ci gaba a Najeriya.

Continue Reading

Labarai

Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Published

on

Wasu manoman tumatur a ƙaramar hukumar Bagwai ta jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.

Manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500. Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.

Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.

”Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,” in ji shi.

Ya yi ƙira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.

KU KUMA KARANTA: Jihar Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma

Haka-zalika, shi ma Sama’ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.

“Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau,” in ji Bello.

Continue Reading

Labarai

Jihar Kebbi za ta raba man fetur kyauta ga manoma

Published

on

Gwamnatin Kebbi ta ɓullo da shiri na musamman domin raba man fetur kyauta ga manoman rani da nufin sauƙaƙa musu yin wahalar noma a jihar.

Kwamishinan Noma na jihar, Shehu Mu’azu ya ce gwamnatin ta samar da haujin noma, inda aka farfaɗo da aikin noma domin jihar ta cigaba da riƙe kambunta a ɓangaren noman shinkafa a Najeriya.

Saboda haka ne ta gina ƙaramin wurin noma na zamani a ƙananan hukumomin Argungu da Fakai a garin Mahuta.

Wannnan a cewarsa, ƙari ne a kan tallafin noman rani da manoman shinkafa 30,000 da masu noma masara 7,500 da kuma masu noman rogo 2,000 suka samu daga gwamnatin.

KU KUMA KARANTA: An ceto manoma 16 daga hannun masu garkuwa da mutane a Neja

Ya ƙara da cewa gwamnatin jiha ta biya kasonta na naira miliyan 350 a cikin shirin RAAMP, wanda zai samar da hanyoyin mota masu tsawon kilo mita 240 domin manoma su samu saukin sufuri, gwamnati ta sanya miliyan 350 a shirin.

Shehu Mu’azu ya sanar da hakan a taron manema labarai na sati-sati da ma’aikatar yada labarai ta shirya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like