‘Yan bindiga a Sakkwato sun kashe ɗansanda da wani
Ana zargin wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in ‘yansanda, Insifekta Eze, da wani ɗan sa kai a Sakkwato a yayin wani kwanton ɓauna da suka kai da sanyin safiyar Litinin.
Lamarin ya faru ne a wani shingen binciken ‘yansanda a mahaɗar Milgoma da ke kan hanyar Sokoto-Bodinga, inda ‘yan bindigar suka kai hari kan jami’an tsaro lokacin da suka kusance su.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufai, ya tabbatar da mutuwar mutanen, yana mai bayyana lamarin a matsayin kwanton ɓauna da aka tsara.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Yobe sun kashe ‘yan Shi’a 3
A wani lamari mai nasaba da wannan, a ranar Lahadi, ‘yansanda sun yi arangama da wata ƙungiyar ‘yan bindiga a kan hanyar Sokoto-Isa, wanda hakan ya haifar da mutuwar ɗaya daga cikin ‘yan bindigar.
A yayin arangamar, an ƙwato bindigar AK-49 daga hannun maharan. ASP Rufai ya tabbatar da cewa za a ci gaba da ba da bayanai yayin da ƙarin bayani.