Yadda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da mutane 53, suka kashe mata masu juna biyu a wasu ƙauyuka huɗu a Neja

3
463

Wata mata mai juna biyu na wata shida da wasu mutane biyar sun mutu sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai wa al’ummar Agwa, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa a yayin harin da aka kai ranar Talata, ‘yan ta’addan, yayin da suke harbe-harbe a cikin al’umma, sun kuma yi garkuwa da mutane 50 zuwa inda ba a san inda suke ba.

Wani ganau mai suna Mallam Audu Muhammad, ya shaida cewa wasu jami’an soji da ke sintiri na yau da kullum a cikin al’umma, sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun garzaya dajin domin gudun tsira.

Audu ya ce, “Yan bindigan sun shigo ƙauyenmu ne suka fara harbe-harbe, mutane suka fara gudu don tsira da rayukansu, kuma an kashe kusan mutum shida.

KU KUMA KARANTA: Yan sanda sun kama dattijo da ke yiwa ‘yan ta’adda maganin bindiga

“A yayin da suke harbe harben, sun kuma kama wasu mutane kuma suka yi gaggawar ficewa daga ƙauyen yayin da sojoji suka iso. “Bisa harbin da sojoji suka yi ya fi karfin ‘yan bindigar, don haka sai ,suka gudu zuwa cikin dajin.

Sama da mutane 50 ne aka yi garkuwa da su, wasu kuma sun samu raunuka yayin da suke tsere wa ‘yan bindigar.” In ji shi.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da jin kai na jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu ba a tantance ainihin adadin waɗanda abin ya shafa ba.

A wani labarin kuma a ranar larabar da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun sace wasu mutane uku daga al’ummar Beji da ke ƙaramar hukumar Bosso a jihar.

Wani shaidan gani da ido, Abdulahi Aminu, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar garin ne da misalin ƙarfe ɗaya na safe, inda suka riƙa harbe-harbe.

“Muna cikin barci sai muka fara jin ƙarar harbe-harbe, sai mutane suka fara gudu cikin daji.

‘Yan bindigar sun shiga ƙauyen suna harbin sama da sa’o’i biyu ba tare da tsayawa ba,” in ji Aminu.

Ya ce an kai harin ne bayan babban asibitin Beji ba tare da ‘yan bindigar sun sami wani ƙalubale daga hukumomin tsaro ko ‘yan banga ba.

Aminu ya ce, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wata mata da ‘ya’yanta mata guda biyu waɗanda kuma suka yi awon gaba da wani a kan haya. Amma daga baya ya tsere.”

Ya ce har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntubi ‘yan uwa ba domin neman kuɗin fansa, bisa zargin cewa sace su na da alaƙa da gadon wani gidan da aka ajiye da ke cikin unguwar Beji.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 cikin dare, inda ya ce an aika da wata tawagar dabaru domin ceto waɗanda lamarin ya shafa.

3 COMMENTS

Leave a Reply