Wasu ‘yan bindiga da suka kai kimanin ɗari biyu a kan babura ɗauke da nagartattun muggan makamai sun kai hari a garin Damari da ke unguwar Kazage da ke Gabashin Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari a Jihar Kaduna.
Bayanai sun nuna cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Laraba 13 ga watan Yuli yayin da ‘yan ƙungiyar Ansaru wato Boko Haram ke cikin garin suna wa’azi ga mutanen yankin. Da jin ƙarar harbe-harbe daga ‘yan bindigar, ‘yan kungiyar Ansaru suka matsa wajensu suka fara musayar wuta.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar masu ci gaba da masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Usman Kasai ya fitar a ranar Juma’a, ya tabbatar da faruwar lamarin.
‘’Sun shafe kusan sa’a guda suna arangama sannan ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda suma dauke suke da muggan makamai suka yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sa suka ja da baya suka gudu,” inji sanarwar.
A yayin arangamar an yi barna a garin, inda aka ƙona shago, motoci biyu, da wani asibiti mai zaman kansa. An kuma bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutane biyu (leburori) a kan hanyarsu ta dawowa daga gona yayin da ‘yan bindigan ke guduwa cikin dajin.
‘’Saboda haka, mafi yawan al’ummar yankin sun yaba tare da jinjina wa ‘yan Ansaru kan yadda suka kare garin daga harin da ‘yan bindiga suka kai musu inda suka yi imanin cewa lamarin zai iya yin illa sosai.
Ɗaruruwan mutane ne wanda suka haɗa da mata da yara ne suka yi hijira daga garin sakamakon harin. A cewar sanarwar, harin ya kasance tsararren, wanda aka yi shiri ne mai tsauri, domin ‘yan bindigar sun san cewa ‘yan kungiyar Ansaru sun mamaye garin. Don haka, ‘yan Ansaru suka yi masa tirjiya.
Sai dai babu tabbas kan adadin asarar da aka samu tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan kungiyar Ansaru. ‘’Yan kungiyar Ansaru na ci gaba da wa’azi da gudanar da shari’a ga mutanen yankin tare da ba su shawarar da su mallaki makamai don kare kansu daga maƙiya tare da yaƙi da Gwamnati domin tabbatar da abin da suke kira daular Musulunci.
Rundunar ‘yan sandan Kaduna ba ta ce uffan ba kan lamarin.