Yadda wani ya kashe abokinsa, ya siyar da sassan jikin ga Fasto da Boka kan naira dubu 200

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba, 2022, ta kama Fasto ɗaya da wasu mutane biyu da laifin yin garkuwa da wani matashi ɗan shekara 39, Adekunle Muyiwa tare da tarwatsa gawarsa domin yin ibada.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin, Idowu Abel, Clement Adeniyi da Fasto Felix Ajadi, an kama su ne biyo bayan rahoton da wani Oluwaseyi ya kai ofishin ‘yan sanda a Owode Yewa a ranar 15 ga watan Nuwamban 2022.

Adekunle, shi ne yayann mamacin,ya ruwaito cewa ƙanin nasa ya bar gida tun ranar 10 ga watan Nuwamba 2022 kuma bai dawo ba tun daga lokacin.

Bayanan da ‘yan sanda suka samu ne ya sa DPO na Owode Yewa, CSP Mohammed S. Baba, ya umarci jami’an ‘yan sandansa da su yi bincike tare da gano musabbabin ɓacewar matashin.

“A binciken da suka yi, sun gano cewa Idowu Abel ne ya zo ya ɗauki matashin daga gidansa a wannan ranar, an kuma gano cewa Idowu Abel nada hannu a ɓacewar matashin.

“Da ake yi masa tambayoyi, Idowu Abel ya amsa cewa wani mai maganin gargajiya ne wanda abokin sa ne ya yaudare shi, aka kai shi gonar Clement Adeniyi, ɗaya daga cikin wanda ake zargin, inda aka kashe shi tare da yanka shi gunduwa-gunduwa.

“Ya kuma ƙara da cewa bokan ya basu tayin ladan Naira dubu 200 idan aka samo masa kai, zuciya, hannu da ƙafafun mutum, ya kuma basu Naira dubu 80 tare da alkawarin biyan ragowar Naira dubu 120 idan suka kawo sassan jikin mutum.

“Bayan ya karɓi kuɗin, Idowu Abel ya je wajen abokinsa Muyiwa Adekunle ya ce ya raka shi wani waje, da yake shi abokinsa ne, wanda aka kashen wanda bai yi zargin wani abu ba ya bi shi, inda ya kai shi gonar Clement Adeniyi inda suka kashe shi suka sassare jikinsa, aka yanke masa kai, da zuciyarsa da sauran abubuwan da sukbuƙata.

Cikin gaggawa suka binne ragowar jikin a wani rami mara zurfi a gonar.”

Bayanan da ya bayar ne yasa a ka kama Clement Adeniyi da Fasto Felix Ajadi, yayin da bokan da aka bayyana da suna Abel ya gudu kuma a halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashen binciken kisan gilla na jihar domin bincike, ya kuma ba da umarnin cewa dole ne a nemo bokan da ya gudu.


Comments

One response to “Yadda wani ya kashe abokinsa, ya siyar da sassan jikin ga Fasto da Boka kan naira dubu 200”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda wani ya kashe abokinsa, ya siyar da sassan jikin ga Fasto da Boka kan naira dubu 200 […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *