Yadda tagwaye biyu da ke manne da juna suka auri mata biyu su kayi ta haihuwa cikin al’ajabi

An haifi Chang da Eng Bunker a nahiyar Siam na ƙasar Thailand a ranar 11 ga watan Mayun 1811, tagwayen da suka shahara a kasar Amurka, inda shahararsu ta sa kalmar “Twins Siamese” ta zama daidai da kalmar tagwaye da ke manne da juna.

Duniya ta ɗaukesu a matsayin abin sha’awa, kuma sun kasance “biyu daga cikin mutanen ƙarni na goma sha tara da aka fi yin nazari ta fuskar nazarin ɗan adam”.

Chang da Eng sun haɗu suka kuma manne da junansu a ƙugu ta wani nau’in jijiya mai tsawon inci 3.25 da fadin kimanin inci 1.5.

Mahaifiyar su ruwa biyu ce, ‘yar ƙasar Sin, mahaifinsu kuma ɗan ƙasar Sin ne, wato ƙasar Chaina.

Mahaifiyarsu ta bayyana cewa haihuwarsu ba ta da bambancin wahala da ta ‘yan uwansu da ta haifa ɗaiɗai da ɗaiɗai.Mahaifinsu Ti-eye, mai kamun kifi ne wanda ya mutu sa’ad da tagwayen ke ƙanana, a lokacin annobar cutar sankarau da ta ratsa yankin a shekarar 1819, babu cikakken bayanai game da rayuwarsu ta ƙuruciya.

Chang da Eng suna da shekaru 17 a lokacin da suka fara yin tafiya zuwa Amurka. Sun isa Boston a ranar 16 ga watan Agustan1829 daga nan sai likitoci da yawa suka fara duba su.

KU KUMA KARANTA: Tarihin Sinan al-Battani, mabuɗin ilmin Taurari

An ba da labarin isowarsu cikin mamaki da alhini a jaridu saboda halittar su da kuma launin fatarsu. Bayan sun bar Amurka, sun zagaya manyan biranen Biritaniya, kuma a lokacin da suka koma New York a watan Maris na shekarar 1831, tagwayen sun sami ƙwarewa a karatu da rubutu da harshen turanci na Ingilishi.

A lokacin da suke yawon shirya wasanni ‘concert’ a birane, tagwayen suna zama a otal, inda suke karɓar kuɗi daga masu zuwa kallon wasan kwaikwayon da sukeyi.

A cikin ƙananan garuruwa kuwa, manajan su yakan aika da wasiƙa kafin isowarsu, kuma suna sauka a masauki na dare ɗaya ko biyu kawai.

Tagwayen suna yin wasan motsa jiki, suna gudu da sauran wasanni masu ƙyatarwa, sukan sa kayan al’ada masu ɗaukan hankali, ayyukansu na lokaci-lokaci sun ƙunshi wasan ninƙaya a ruwa, wasan duba na rufa ido, da kuma yin wasan kwaikwayo.

A cikin shekarar 1843, Chang da Eng sun yi aure inda suka auri ‘yan uwan juna Adelaide da Sarah Yates, ‘ya’yan wani fitaccen mutum na wancan lokacin mai bada gidajen haya a Amurka.
Ko da yake ’yan matan suna da masoya da yawa, tagwayen sukan kai mu ziyara akai akai na tsahon shekaru, suna ziyartarsu sa’ad da suka dawo daga balaguron kasuwanci, kuma ta haka suka saba da dukan surukansu har aka kai ka ɗaura masu aure da su.

Ma’auratan sun kasance iyalai biyu babu shakka, amma suna zauna a cikin gidaje daban-daban, tare da matansu, suna raba mako a tsakaninsu, kowa tare da matarsa.

Haka zalika ko wacce mace ta haihu a a shekarar 1844. Duk da yake babu cikakken bayani game da yadda ma’auratan suke gudanar da al’amuran da suka shafi zaman aurensu, abin ƙayatarwa shine yadda matansu sukayi haihuwar farko kwanaki shida a tsakani, a haihuwa ta biyu, babancin ƙwanaki takwas.

Suka kuma ci gaba da samun ‘ya’ya a tsakanin su wanda sun kai 21 cikin ban mamaki.

A farkon Oktoba 1860, sun rattaba hannu tare da shahararren ɗan wasan kwaikwayo PT Barnum na wata ɗaya kuma sun baje kolin a gidan tarihin Barnum’s na ƙasar Amurka da ke birnin New York, inda suka yi wa manyan baƙi da yawa wasansu da barkwancinsu, ciki har da Yariman Wales.

A lokacin da yakin basasa ya ƙare a shekara ta 1865, dukiyar tagwayen tayi ƙasa inda ta rabu ƙwarai don haka suka yanke shawarar ci gaba da yawon wasan Barkwanci.

Chang da Eng sun yi tafiya zuwa Biritaniya a cikin shekarun 1868-69, inda suka dingi ganawa da likitoci da kuma yawon buɗe-ido, domin rabonsu da Ingila ya kasance sama da shekaru 30 a baya.

‘Yar Chang Nannie, wacce ba ta taɓa yin nisa da gida ba, da ‘yar Eng Kate, dukkansu ‘yan shekara 20, su ma an yi wannan tafiya da su.

A cikin shekarar 1870, Chang ya yi fama shanyewar jiki ta gefen damansa, gefen da ke kusa da ɗan’uwansa Eng, hhakanbne yasa ɗan uwan nasa yake tallafa shi, yayin da Chang ya daure kafarsa ta dama a cikin majajjawa kuma yana amfani da sandar guragu da hannun dan uwansa, yana gudanar da ayyukansa na yau da kullun a haka, Amma bai samu cikakkiken koshin lafiya ba, ya kuma kamu da mugun tari, kawai sai ya faɗa shaye shaye.

Da sanyin safiya na ranar 17 ga watan Janairun1874, ɗaya daga cikin ‘ya’yan Eng ya duba tagwayen suna barci, sai ya ce “Kawu Chang ya mutu,” yaron ya ke faɗawa mahaifinsa Eng, wanda ya amsa masa da cewa “to ni ma binsa zanyi!

Nan da nan bayan mutuwar Chang, Eng ya shiga matsanancin wahala da damuwa, gumi mai sanyi ya rufe jikinsa.

Iyakar abin da ya iya yi bayan rasuwar ɗanuwansa shine ya matso da jikinsa kusa da shi, kuma sa’o’i biyu da rabi bayan rasuwar ɗan’uwansa, Eng Bunker ya rasu.

Tagwayen biyu da ke manne da junansu sun rasu sunada shekaru 62 a duniya.


Comments

2 responses to “Yadda tagwaye biyu da ke manne da juna suka auri mata biyu su kayi ta haihuwa cikin al’ajabi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda tagwaye biyu da ke manne da juna suka auri mata biyu su kayi ta haihuwa cikin al’ajabi […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Yadda tagwaye biyu da ke manne da juna suka auri mata biyu su kayi ta haihuwa cikin al’ajabi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *