Yadda sojoji suka harbe yaro ɗan shekara 15, da ɗan adaidaita a Legas

0
442

A baya-bayan nan dai wani bala’i ya afku a jihar Legas yayin da ake zargin sojoji da ke aiki da rundunar ‘Operation MESA’ sun harbe wani yaro ɗan shekara 15 mai suna Pelumi Sulaimon da wani mai tuƙin babur mai ƙafa uku, mai suna Aloma.

Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, wasu ‘yan bangar siyasa ne suka ɗauko hayar sojojin domin aiwatar da ramuwar gayya ga abokan hamayyar su a ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu.

Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa sojojin sun isa ne a cikin wata mota kirar motar da aka rubuta OP MESA inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.

Pelumi, wanda ke kan hanyarsa ta sayo wa abokansa abubuwan sha don murnar zagayowar ranar haihuwarsa,harsashi da sojin suka harba na kan mai uwa da wabi ya sake shi.

KU KUMA KARANTA: Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe

A ɗaya bangaren kuma, maharan sun yi kuskuren cewa Aloma matuƙin babur mi ƙafa uku ɗaya ne daga cikin waɗanda suke nema inda shima suka harbe shi.

Lamarin dai ya samo asali ne sakamakon rikicin siyasa a tsakanin ɓangare biyu da basa ga maciji ga juna.

Rikicin dai ya faru ne a daren ranar Alhamis kuma an sasanta ɓangarorin bayan da wasu mazauna yankin suka shiga tsakani.

Sai dai an sake samun wata arangama tsakanin jam’iyyun siyasa a lokacin zaɓen da aka gudanar a ranar asabar, kuma a ranar lahadin da ta gabata ne wani ɗan daba na ɗaya daga cikin jam’iyyun siyasar ya kawo sojoji inda suka kutsa kai cikin sansanin da rikicin ya afku a karo na ƙarshe.

Lokacin da suka isa wurin, ba su ci karo da waɗanda suka kai musu hari ba, don haka sojojin na OP MESA suka fara harbi ba kakkautawa, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar Pelumi da Aloma.

Yayan Pelumi, Afeez, ya ce yana tare da abokansa ne sai wani mazaunin yankin ya shaida masa cewa sojoji sun harbe ɗan uwansa, inda ya sauko da sauri ya ga ƙanwarsa na kokarin ɗaga Pelumi daga ƙasa.

Sun kai shi asibiti, amma ya rasu, inda aka ɓukaci da su sami rahoton ‘yan sanda kafin su ɗakko gawar, don haka ‘yan sandan suka ɗauke gawar daga asibitin suka ajiye a dakin ajiyar gawa.

Lamarin dai ya jefa iyalan Pelumi da ɗaukacin al’ummar yankin cikin makoki. Pelumi ya cika shekara 15 a ranar da aka harbe shi, kuma yana ɗokin yin bikin cikarsa shekaru 15 tare da abokansa lokacin da aka kashe shi, inda harsashin sojojin da ya kamata su kare shi ya katse rayuwarsa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce lamarin yana hannun hukumar binciken manyan laifuka ta jihar. Sai dai har yanzu ba a kama wanda ake zargi ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Ba a samu jin ta bakin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na runduna ta 81 ta sojojin Najeriya Olabisi Ayeni, domin bai amsa sakon tes da aka aika zuwa lambar wayarsa ba har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoto.

Leave a Reply