Yadda na kawo karshen yajin aikin ASUU cikin kwana ɗaya aya – Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana yadda gwamnatinsa ta shawo kan yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU na tsawon wata huɗu a cikin kwana ɗaya lokacin mulkinsa.

Jaridar Daily Trust ta ce Jonathan ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a Abuja, yayin bikin cika shekara 70 na Bishop Mathew Hassan Kuka, shugaban babban cocin katolika ta Sokoto wadda cibiyarsa ta shirya.

Tun wa watan Fabrairu ne malaman jami’a suka fara yajin aiki kan wasu bukatu da gwamnatin tarayya ta kasa biya musu.

“Al’ummar da muke rayuwa a cikinta na da fadi, muna magana a kan yajin aiki ASUU, lokacin da nake mulki, ASUU ta shiga yajin aiki na wata hudu, kwamitoci daban-daban sun yi zaman tattaunawa amma ba a samu mafita ba,” in ji Jonathan.

Tsohon shugaban ya ce da suka ga abun yana nema ya gagara, sai shi da mataimakinsa tare da babban Atoni Janar da sakataren gwamnatin tarayya da ministan ilimi suka jagoranci wani zama, inda a cikin daren aka cimma yarjejeniya da ASUU.

“Da farko na dauka saboda zuwana wajen za a daidaita a kan lokaci, sai dai mun shafe tsawon dare muna tattaunawa kafin mu ƙarƙare da kuma janye yajin aikin da 5:30 na safe,” a cewar Jonathan


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *