Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta

Hukumar hana fataucin mutane ta ƙasa reshen jihar Anambra tare da haɗin gwiwar ‘yan banga sun cafke wasu mutane uku da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade.

Mutane huɗu ne ake zargi da hannu a lamarin, amma zuwa yanzu mutum uku aka kai ga kamawa yayin da ake neman na huɗun ruwa a jallo bayan da ya tsere a lokacin da jami’an tsaro suka mamaye unguwarsu da ke Nkpor, kusa da garin Onitsha, a jihar Anambra.

Kwamishiniyar mata da zamantakewa ta jihar, Ify Obinabo, ta bayyana wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba a Awka ta hannun mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Chidimma Ikeanyionwu. Ta ce an mika masu laifin ga hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Awka, za Kuma a gurfanar da su gaban kuliya, ta kuma bada tabbacin za a tabbatar da adalci.

A yayin da ake yi wa waɗanda ake zargin tambayoyi, biyu daga cikin waɗanda ake zargin sun amsa laifin da suka aikata tare da neman gafara, inda suka ce sun yi wa yarinyar fyaɗe ne saboda rashin jituwa da ke tsakaninsu mahaifinta wanda suke zargin yayi masu laifi, amma na ukun su ya ce bai yiwa yarinyar fyaɗe ba, sai dai yana wajen a lokacin da aka yi mata fyaɗen. Saɓanin iƙirarin nasa, yarinyar da aka yima fyaɗen ta shaida cewa shi ne mutum na biyu da yayi lalata da ita.

A cewarta, waɗanda ake zargin na zaune a gidan da mahaifinta ke haya ne, kuma sunyi mata fyade bayan sun samu saɓani da mahaifin nata.

Da take ba da labarin abin da ya faru, yarinyar ta ce da farko sai da suka kwaɗa mata mari, sannan suka ja ta zuwa wani waje, sannan suka umarce ta da ta cire tufafinta yayin da waɗanda ake zargin suka yi mata fyaɗen ɗaya bayan ɗaya.


Comments

3 responses to “Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Yadda mutum huɗu suka yi wa Yarinya fyade saboda laifin babanta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *