Wata mata mai suna Okereke Olufunmilayo, wacce ita ce manaja a wani kantin sayar da kayan gini, tare da mijinta da ɗan aikinta an kama su da laifin yin garkuwa da daraktan Otal din Rolak da ke Ijebu-Ode a Jihar Ogun, mai suna Otunba Abayomi Ajayi Smith.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Ogun matar ta aikata wannan aika aika ne tare da taimakon mijinta, Larry Adebayo Adewumi, da kuma yaron ɗakinta da ke taya ta aiki mai suna Adebowale Sanni.
Yace ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikacin otal ɗin ne a ranar 28 ga Satumba, 2020, da misalin ƙarfe 7:30 na safe a rukunin gidajen na Anifowose da ke yankin Igbeba a Ijebu-Ode.
Bayan da suka sace manajan hotel ɗin sun kuma kashe shi duk da sun karɓi kuɗin fansarsa Naira miliyan goma sha biyar.
Tun a wancan lokaci jami’an ‘yan sanda ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen bankaɗo waɗanda suka yi garkuwar tare da kisan ma’aikacin Otel ɗin.
Abimbola Oyeyemi, ya ƙara da cewa ƙoƙarin da rundunar ‘yan sandan jihar ya haifar da nasara a watan Satumban wannan shekara, inda suka samu labarin masu garkuwar na shirin sace mata da ɗan waɗanda suka kashe tun da farko.
Yayin da rundunar ta fara aikin sa ido kan waɗanda ake zargin, ɗaya daga cikinsu mai suna Adebowale Sanni mai shekaru 55, an gano shi a yankin Ikeji Arakeji a jihar Osun, inda nan take aka kama shi.
Yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya furta cewa shidai umarni aka bashi na ya bi matar mai suna Olusola Roseline Ajayi, wanda umarnin yazo ne daga Larry Adebayo Adewumi shugaban ƙungiyar, wanda matarsa, Olufunmilayo ma’aikaciyar Otunba Ajayi ce.
Ya kuma ƙara da cewa Larry ne ya bayyana ma sa inda otal ɗin wanda aka kashen yake da sauran kayan kasuwancinsa tare da ba shi umarni cewa idan har suka yi nasarar yin garkuwa da matar da ɗanta to dole ne a kashe su biyu bayan sun karɓi kuɗin fansa domin kada su bar wata alama da za a gano su, kamar yadda suka yi wa mijinta shekaru biyu da suka wuce, kama shin da akayi yasa a ka kai ga kama Olufunmilayo da mijinta.
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa Larry, ɗan asalin garin Ilesha na jihar Osun, ya taɓa zama ɗan damfara kafin ya shiga sana’ar satar mutane na.
“Hanyar aikin da ya yi shi ne ya nemo wani attajirin da aka kashe, daga nan ne ya haɗa gungun ‘yan kungiyar da ke yi masa aiki, Larry ya samu cikakken bayani game da marigayi Otunba Ajayi ta hannun Olufunmilayo, wadda ita ce manajan marigayin.
“Bincike da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Larry yana da asusu guda biyu na banki, “inda yake ajiyar kuɗaɗen da ya samu ta hanyar aikata laifuka.”
Oyeyemi ya kara da cewa cewa wanda ake zargin yana da asusun bankin Jaiz mai lamba 0010913206, da kuɗi N34,953,455. Haka kuma asusun ajiyar sa na bankin Access yana da kudi N4,576,846.
An kuma gano wata mota ƙirar Toyota Highlander 2014 daga hannunsa.
Da yake yabawa tawagar ‘yan sandanbda suka yin aikin kama wanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole ya bayar da umarnin a zakulo sauran ‘yan ƙungiyar tare da gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
[…] KU KUMA KARANTA:Yadda mata da miji sukayi garkuwa, tare da kashe mai hotel bayan sun karɓi kuɗin fansa miliyan 15 […]
[…] KU KUMA KARANTA:Yadda mata da miji sukayi garkuwa, tare da kashe mai hotel bayan sun karɓi kuɗin fansa miliyan 15 […]