Mutane 37 sun mutu a hatsarin mota tsakanin Damaturu zuwa Maiduguri

2
280

Daga Ibraheem El-Tafsir

A ƙalla mutane 37 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya auku a tsakanin hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, a ranar Talata.

Haɗarin ya rutsa da motoci ƙirar Hummer guda biyu da Gulf guda daya waɗanda suka hadu a daidai ƙauyen Jakana, inda nan take motocin suka kama da wuta.

Mutane 37 ne suka mutu, 8 kuma sun samu munanan raunuka,kuma suna karbar magani a Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Shugaban hukumar kiyaye hadɗurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Borno Utten Iki Boyi ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Tuni dai aka yi wa wadanda suka mutu sutura a kabarin bai daya, sakamakon konewar da suka yi kurmus.

2 COMMENTS

Leave a Reply