Yadda Fela ya auri mata 27 a rana guda a Legas

0
289

A shekarar 1978, majagabam kiɗan Afrobeats, Fela Anikulapo Kuti, ya auri mata 27 a rana ɗaya, wannan ba abin mamaki bane ga waɗanda suka san rayuwa da salon na fitaccen mawaƙin Najeriyar da ake yi wa laƙabi da yaren Yarbanci da Abami Eda, wato halitta me ban mamaki.

An haifi Olufela Olusegun Oludotun Ransome-Kuti, a ranar 15 Oktoban 1938, ya rasu a 2 ga Agustan1997, sannan ana masa laƙabi da Abami Eda, mawaƙin Najeriya ne, makiɗi, ɗan gwagwarmayar siyasa, kuma ɗan kishin Afrika.

Ana ɗaukansa a matsayin majagaba na kiɗan da waƙe na Afrobeat, nau’in kiɗan Najeriya wanda ke haɗa kiɗan Afirka ta Yamma da funk na Amurka da jazz.

KU KUMA KARANTA: Tarihin Ali Jita da waƙoƙinsa

A lokacin da ya yi fice, an kira shi a matsayin ɗaya daga cikin “mawallafan kaɗe-kaɗe da kwarjini a Afirka”. All Music sun bayyana shi a matsayin muryar kiɗa da siyasa mai mahimmanci ta duniya.

Mahaifiyar Femi Kuti ta kasance ‘yar fafutukar kare haƙƙin matan Najeriya, Funmilayo Ransome-Kuti. Bayan samun ƙwarewa da horo a ƙasashen waje, shi da ƙungiyarsa ta Afirka 70 (wanda ta haɗa da daraktan kiɗa Tony Allen) sun yi rawar gani da nuna bajinta a Najeriya a cikin shekarun 1970s, a lokacin ya kasance mai sukar lamirin gwamnatin mulkin sojan Najeriya.

A cikin 1970, ya kafa ƙungiyarJamhuriyar Kalakuta, wacce ta ayyana kanta a matsayin bijirewa daga mulkin soja. Anyi fata -fata da yankin a cikin wani hari na 1978.

Da yawa daga cikin ‘yan ƙungiyar sun zama marayu, da kuma zawarawa marasa galiho, domin ya haɗa su tare, Fela ya yanke shawarar yin abin da ba a saba gani ba, inda ya bai wa mata ’yan ƙungiyar sa takarda domin rubuta sunayen waɗanda suke son aurensa; gaba ɗaya ‘yan ƙungiyar mata 27 suka rubuta sunayensu.

Bayan samun yardarsu, Fela Kuti ya auri matan su 27 a ranar 20 ga Fabrairun 1978, a otal ɗin Parisona da ke Anthony a Legas, tare da sanya albarkar limaman tsafi na Ifa su goma sha biyu.

Iyayen wasu daga cikin matan sun nuna damuwarsu da auren. Fela ya auri matan ne domin ya kula da su tare.

Ɗaurin auren ya samu halartar dangin Fela da abokansa da sauran ’yan ƙungiyar, kuma yayin daurin auren, Fela ya yi gajeriyar jawabi, inda yayi liƙin kuɗi a goshin matan nasa sannan ya ba su takardar shaidar auren.

Fela ya raba kwana a tsakanin matan nasa, wanda ya ƙunshi mata 12 a lokaci guda. Bayan daurin auren, Fela ya ɗauki matansa su 27 zuwa ƙasar Ghana domin hutun ma’aurata.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kama Fela a shekarar 1984, ta ɗauresa, amma bayan wata 20 ta sake shi.

Sai dai a shekarar 1986, jim kaɗan bayan fitowarsa daga gidan yari, Fela Kuti ya saki matansa guda 27 bisa dalilin cewa aure yana kawo kishi.

Wani abin lura da birgewa shine babu wadda Fela ya tilasta wa barin gidansa bayan sakin, wasu sun zauna tare da shi har ya rasu a shekarar 1997.

Tun mutuwarsa a cikin 1997, ɗansa, Femi Kuti ne ke kula da sake fitowa da kuma harhaɗa wakokinsa.

Leave a Reply