Connect with us

Gwamnatin Tarayya

Yadda Buhari ya ƙaddamar da ayyukan Gwamna Buni na jihar Yobe

Published

on

A ranar Litinin ne Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci jahar yobe domin ƙaddamar da ayyukan bilyoyin kuɗaɗe Wanda gwamnan jihar Mala Buni yayi a faɗin jihar.

KU KALLI HOTUNAN ANAN: https://youtu.be/PeoxYImZEKo

Ayyukan sun haɗar da buɗe tashar jirginsa ta kaya wato Cargo Airpot wanda aka sanya sunan Shugaba Muhammadu buhari, daga bisani aka buɗe sabon asibitin horaswa wanda ya ƙunshi ɓangaren karbar haihuwa na asibitin wanda yana cikin mafi girma a faɗin Africa, an samar da dukkan wannan ayyuka ne a birnin damaturun jihar yobe.

Sannan ya kaddamar da buɗe sabuwar kasuwar zamani mai suna Ibrahim Gaidam Ultra Modern Market wacce take da shaguna fiye da ɗari bakwai wanda gwamna Buni ya gina domin bunƙasa hanyar kasuwanci a birnin Damaturu dama faɗin jihar yobe.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/76GsZBj0l3E

Akwai ire-iren wa’annan ayyuka na bilyoyin ƙudaɗe wanda gwamnan ya keyi a faɗin jahar yobe musamman garin Nguru, Gashua da kuma birnin Potiskum in da ake gina musu sabuwar kasuwar zamani da kuma katafaren wajen fakin manyan mototi (trailer park).

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: INEC ta fara raba muhimman kayayyakin zaɓe a Yobe | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Gwamnatin jihar Yobe ta fara aikin tituna da magudanan ruwa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Gwamnatin Tarayya

Gwamnatina za ta ba da fifiko kan walwalar mata-Tinubu

Published

on

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, ya sha alwashin cewar gwamnatinsa za ta ba da fifiko kan walwalar mata da kiyaye haƙƙoƙinsu tare da bunƙasa rayuwarsu.
A sanarwar da hadiminsa akan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar game da zagayowar ranar mata ta duniya, Tinubu ya bayyana mata a matsayin ƙashin bayan ci gaban kowace al’umma.

Shugaban ƙasar wanda ya fayyace irin rawar da mata ke takawa wajen gina al’umma, ya jaddada cewar, babu shakka, matan Najeriya sun ba da gudunmowa wajen bunƙasa, ci gaba da kuma ɗaukakar ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Najeriya za ta fara amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar ‘yan bindiga

A cewar sanarwar, “Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewar a kowane ɓangare na ci gaban ɗan adam, irin zarar da matan Najeriya suka yi shaida ce ta jajircewa da ƙarfin hali da fikira ta dukkanin matan duniya, kuma wata alama ce ta nagartaccen wakilci na kyakkyawan fata da wanzuwar al’amura.

Tinubu ya ƙara da cewar, taken bikin ranar mata ta duniya na bana na, “a zuba jari a mata domin hanzarta ci gaba”, ya dace da manufofin da gwamnatinsa ta ƙirƙira akan ilimi da baiwa mata tallafi, ba wai kawai ta hanyar shigo da su a harkar mulki ba, harma da tabbatar da cewa sun ci gaba da zama murya mai mahimmanci a fannin ci gaba a dukkanin ɓangarorin tattaliin arziƙi.

Hakazalika Shugaba Tinubu yace, “gwamnatinsa ta maida hankali wajen zuba jari a fannin ilmin ‘ya’ya mata, tare da ƙirƙirar tsare-tsaren da za su ƙarfafesu wajen ba da gudunmowa a fannonin ilmi da kimiya da fasaha da bincike da ƙirƙire-ƙirƙiren da za su yi tasiri a nan gaba”.

Continue Reading

Gwamnatin Tarayya

Matakan da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na ƙayyade farashi ba zai kawar da yunwa ba – Masana

Published

on

Masana tattalin arziƙi a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka da ƙyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo ƙarshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da buɗe iyakoki domin shigowa da abinci cikin ƙasar ba.

‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin ƙasar.

Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ɗaukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin ƙasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila.

To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati.

KU KUMA KARANTA:Tsadar abinci: Gwamnati za ta fara raba kayan abinci a faɗin Najeriya – Kwamiti

Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai waɗanda ke sayen kayan abinci a ƙauyuka, domin sayarwa da tsada, haka kuma dole a karya farashin kayan masarufi da dawo da darajar Naira.

Ko a makon da ya gabata sai da wata kotun tarayya da ke jihar Legas ta umarci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki ƙwararan matakai na kawo ƙarshen hauhawar kayan masarufi na kafa hukumar ƙayyade farashin abinci ta kasa.

Wasu ‘yan Najeriya sun cewa akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki mataki na dawo da darajar Naira da bunƙasa noma da tattalin arziƙi dama dawo da tallafin man fetur.

A ɓangarensa dai Farfesan harkar Noma Abubakar Gudigi cewa ya yi akwai matakin da gwamnati ya kamata ta ɗauka na hana manyan ‘yan kasuwa shiga ƙauyuka domin saye kayan gona daga manoma.

Yanzu dai a yayin da gwamnati ta ɗauki matakai na rage farashin kayan abinci, abun jira a gani shi ne ko matakan za su taimaka wajen kawo sauƙi ga ‘yan ƙasa.

Continue Reading

Gwamnatin Tarayya

Da ba a cire tallafin mai ba, da wahalar da za’a sha a Najeriya ta fi ta yanzu – Gwamnatin tarayya

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.

A lokacin jawabinsa na farko bayan rantsuwa, a Abuja, a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.

KU KUMA KARANTA: Za’a rufe kasuwar canji a Abuja, har sai abin da hali ya yi

Tun daga lokacin da shugaban ya sanar da janye tallafin man kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta ƙara tsada ga jama’a.

Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a ƙasar a lokacin a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanarwar cirewar farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like