Yadda alayyahu ke taimaka wa jikin ɗan Adam

0
638

Alayyahu wani koren ganye ne da ake amfani da shi a sassa daban-daban a faɗin duniya wanda kowa na iya saye saboda rashin tsadarshi. Ya kuma samo asali ne daga dangin abinci da turawa ke kira Amarantaceae.

Wannan ganye ya ƙunshi sunadaran gina jiki da inganta lafiyar ɗan Adam da suka hadar da; niacin, zinc, protein, folate, calcium, iron, beta-carotene, luthene, xanthene, chlorophynyll, magnesium, phosphorus, potassium, copper da kuma manganese.

KU KUMA KARANTA:Abincin Najeriya da masu neman haihuwa ya kamata su ci

Masana kiwon lafiya suna shawartar al’umma da su yi riƙo da wannan ganye a mu’amalolinsu na yau da kullum domin yin abinci, sakamakon wannan sunadarai da ya ƙunsa domin inganta lafiyar jiki da suka hadar da;

  1. Inganta ƙarfin gani sakamakon sunadaran beta-carotene, luthene da xanthene. Wannan sunadarai su na kuma warkar da cututtukan idanu na ɗan Adam.
  2. Sinadaran folate, potassium da antioxidants dake ƙunshe a cikin alayyahu su kan kawar da cutar kwalkwalwa da a turance ake kiranta Alzheimer’s.
  3. Alayyahu na kawar da cutar hawan jini tare da bude tashoshin da magudanan jini, ya na kuma kawar da cututtukan zuciya.

Ganyen Alayyahu ya ƙunshi sinadaran vitamin K, manganese, zinc, copper, phosphorus da kuma magnesium da suke inganta ƙarfin ƙashi na jikin ɗan Adam.

  1. Alayyahu na bada kariya da kuma warkar da cutar gyambon ciki wato Ulcer.
  2. Sinadaran folate, tocopherol da kuma chlorophyllin da ake cikin alayyahu su na warkar tare da bayar da kariya ga cutar daji musamman ta mama na mata da hanji na cikin ɗan Adam.
  3. Alayyahu na kare fatar ɗan Adam daga cututtuka.

Leave a Reply