Yadda aka kashe mijina Musulmi, mahaddacin AlKur’ani, kan zargin yi wa Annabi ɓatanci’

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Batun ɓatanci ga addini a sassa daban-daban na duniya wani batu ne mai sarƙaƙiya da ke bukatar taka-tsantsan. Addinai da Ƙasashe na da dokokin hukunta ɓatanci ga addini.

A ƙasashen da ke bin tsarin shari’ar Musulunci, an tanadar da hukuncin kisa. A jihohi da dama na arewacin Najeriya ma – inda ake amfani da tsarin na shari’ar musulunci da kuma dokokin Ƙasa a lokaci guda – an tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi ɓatanci ga addinin Islama.

To amma wani batu da a baya-bayan nan ke sake janyo cece-ku-ce da tayar da jijioyin wuya shi ne yadda wasu fusatattun mutane kan far wa waɗanda aka zarga da yin ɓatanci ga addinin Islama.

Aƙalla mutane biyu ne aka kashe a yanayi mai sarƙaƙiya a baya-bayan nan. An kashe wata ɗaliba kirista a Sakkwato mai suna Deborah Emmanuel, da kuma wani matashi musulmi mai suna Ahmad Usman a Abuja babban birnin kasar.

BBC ta zanta da iyalan wadanda lamarin ya shafa kan halin da suka shiga – da kuma malaman addinai kan wannan batu.

“Kun cuce ni, kun cuci rayuwata”

Ba mabiya addinin Kirista ne kaɗai fusatattu kan far wa ba dangane da batun ɓatanci ga addini.

Cikin watan Yuni, wasu wadanda suka harzuƙa sun far wa wani matashi Musulmi mai suna Ahmad Usman, suka lakaɗa masa duka, suka kashe shi, kana suka ƙona gawarsa bisa zargin cewa ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci.

Lamarin ya faru ne a unguwar Lugbe da ke Abuja babban birnin Najeriya.

Na ziyarci gidansu Ahmad, inda na tarar da ƴan uwa da abokan arziki na cikin jimani – cikinsu har da matarsa Zainab, mai zaman takaba.

Watansu takwas da aure kafin a kashe shi. Tana da juna biyu, tana fatan samun ɗansu na fari kuma na ƙarshe.

Zainab na zub da hawaye, dangi na rarrashinta. Ta musanta zargin da aka yi wa mijin nata, tana mai cewa ƙazafi ne.

Ahmad mai shekaru 30 da haihuwa, ɗan banga ne.

Bayanai sun nuna cewa yayin da Ahmad ke sintiri, sai suka yi jayayya da wani malamin addinin Musulunci kan buƙatar malamin ya kiyaye dokar hana fita da dare.

Daga nan Malamin ya zarge shi da yi wa addinin Musulunci ɓatanci. Washegari kuma fustattun suka kashe Ahmad a kusa da ofishin ƴan bangar. Abokan aikinsa sun ce zaƙaƙurin ma’aikaci ne.

Abokan aikin Ahmed Usman

“Wannan ƙazafi da suka yi masa, shi ne ya fi damuna a zuciya’’ a cewar Zainab.

“A kullum mijina ba shi da wata magana sai dai ka ji ya ce ‘mu yi wa Annabi salati’ kuma shi mutum ne da ya haddace Alkur’ani a kansa.”

Ta haƙiƙance cewa babu yadda mai gidan nata zai yi wa Annabi ɓatanci.

Mai dakin Ahmad ta ce saboda irin yadda take jin zafin wannan “ƙazafi” ba za ta yafe wa wadanda suka kashe mata miji ba – amma ta roki Allah “Ya shiryi masu irin wannan hali’’ na ɗaukar doka a hannu ba tare da hujja ba.

“Sun cuce ni, kuma sun cuci iyayensa’’ in ji matar mai juna biyu. Ta yi imanin jajircewarsa a kan aiki ne ya aka yi masa “sharri” kuma lamarin ya kai ga kashe shi.

Zainab ta ce a marainiya ta taso, iyayenta sun rasu tun tana jaririya.

Tana ɗaukar mijin nata tamkar “uwa da uba” saboda yadda yake kula da ita yana kuma tausaya mata, yana share mata hawaye.

Ta ce wadanda suka kashe shi “sun cuce ni, sun cuci iyayensa” kuma yanzu “ban san yadda rayuwa zata kasance mini ba.’’


Comments

One response to “Yadda aka kashe mijina Musulmi, mahaddacin AlKur’ani, kan zargin yi wa Annabi ɓatanci’”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda aka kashe mijina Musulmi, mahaddacin AlKur’ani, kan zargin yi wa Annabi ɓatanci’ […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *