Ya lakaɗa wa matarsa duka, a kan ta fita ba da izininsa ba

0
320

Wani magidanci a jihar Zamfara, ya lakaɗa wa matarsa duka, ya farfasa mata jiki, ya kumbura mata idanu a kan ta fita ba da izininsa ba. Matar mai suna Habiba Mustapha, mai shekaru 27, wadda take unguwar Toka, ta kai kuka wajen ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasa, a kan a ƙwata mata ‘yancinta.

Ta ce mijin nata, ma’aikacin kotu ne, kuma bai taɓa aure ba, ita ce matarsa ta fari. Amma ita taɓa aure kafin ta aure shi. Kuma watansu tara ne da auren. “Daga saɓa ni ya haɗa mu da shi sai ya hau duka na, amma bai taɓa min irin wannan dukan ba” inji ta.

Habiba ta shaida wa ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasa, reshen jihar Zamfara cewa “abin da ya haɗa mu shi ne, na ce masa zan fita na kai cajin waya, sai ya yi shiru, idan ya yi shiru alamar na tafi kenan. Sai na tafi na kai cajin a maƙwabta, shi kuma ya fita, ya tafi masallaci. Bayan na dawo daga kai cajin, sai na samu ya rufe ƙofofin ɗakunan. Ina ta tun ƙarfe 5:00 na yamma, har sai 11:00 na dare ya dawo. Da ya dawo, sai ya kwanta a falo, ni kuma na shiga ɗaki na kwanta”.

KU KUMA KARANTA: Yadda za a magance yawan kwanciyar gaban ɗa namiji yayin saduwa da iyali

“Da Asuba sai ya tafi masallaci, bayan ya dawo daga sallah, sai ya doki ƙofar ɗakin da ƙarfi, har sai da labulen ɗakin ya faɗo. Da naga labulen ya faɗo, sai na tashi zan gyara labulen, na ɗauka labulen ne ba ya so. Kawai sai na ji ya hauni da duka. Yana ta duka na har na rasa inda kai na yake. Can sai na farfaɗo, sai na ga maƙwabtanmu sun shigo, sun samu ya maƙure min wuya na, ina numfashi da ƙyar. Da ƙyar suka ƙwace ni a hanunsa. Sai ya ce ya sake ni, saki ɗaya”

“Ni dai ban san laifin da na masa ba, amma shi yana cewa, wai na fita ba da izininsa ba. Kuma ai daman ina fita, musamman idan bai bar min abinci ba. Sai na fita na sayo abinci na ci”.

Yaya aka yi idonki ya yi ja kuma ya kumbura haka?

Dukan idon ya dinga yi da hanunsa, yana caccaka yatsunsa a ciki. Daman ya ce ba zai sake ni ba, sai ya yi illa wadda zan fita da ita.

Ko kin sanar da ‘yan sanda a lokacin da abin ya faru?

Eh akwai maƙwabcinmu Nura, shi ne ya je ya sanar da ‘yan sanda, sai suka taho tare. Sai muka tafi ofishin ‘yan sanda. Bayan mun je ofishin ‘yan sanda, sai ya gaya musu abin da na masa, wai na fita ba da izininsa ba. Sai babban ‘yan sanda ya ce “abin da ta yi maka, bai kai ka yi mata wannan duka ba”. Bayan an tattauna, sai yayana ya zo ya yi belina. Shi kuma a hanun ‘yan sanda ya kwana, sai da safe aka ba da belinsa. An kai ni Asibiti, an ba ni magunguna ina sha. Amma har yanzu jikina duk ciwo yake. Sannan ido na ji nake kamar an watsa min ƙasa a ciki.

“Ina so wannan ƙungiya ta kare haƙƙin ɗan’Adam, ta ƙwata min haƙƙina, na irin cin zarafi da lahanta ni da ya yi da duka. Sannan a ƙwata min kuɗi na a hanunsa, naira dubu 41, wanda na ba shi aro ya kuɗin haya” inji Habiba.

Kwamared Salisu Umar, shi ne shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasa (mai zaman kanta) reshen jihar Zamfara. Bayan ya saurari koken Habiba, ya ce “wannan rashin adalci ne, kuma ya aikata hakanne da gangan. Yanzu da a ce wannan ɗin ƙanwarsa ce, ko ‘yarsa aka mata haka ba zai ji dadi ba. Sannan kuma abin mamaki shi ne yadda ‘yan sanda suka kashe ‘case’ ɗin ba tare da ɗaukar mataki a kan mijin ba. Yanzu ka duba waɗannan idanun nata za su iya mutuwa. Lallai ‘case’ ɗin bai mutu ba. Yanzu na kira ‘central Police station’ na ce a buɗe ‘case’, a cika ‘file’ a tura ‘case’ ɗin kotu, don a bi mata haƙƙinta.

“Kuma daga yanzu a shirye muke mu ba ta lauya, saboda muna da lauyoyi masu zaman kansu, ƙarƙashin jagorancin Barista Bello Umar. Chamner ɗinsa a tsaye take wajen ba mu gudumawa a jihar Zamfara. Haka ma chamber ɗin Barista Wali da Barista Safiyanu a shirye suke su ba mu gudumawa kyauta ga wanda aka zalunta”. Inji shi

Leave a Reply