Wata ‘yar Brazil ta haifi tagwaye tare da ubanni biyu daban-daban

0
238

Wata mata ‘yar Brazil ta cika kanun labarai bayan da tagwayenta suka tabbata ‘ya’yan mutum biyu ne daban-daban a gwajin DNA, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Globo ta ruwaito.

Wannan wani sabon yanayi ne da ake kira ‘heteropaternal superfecundation’. Yana faruwa ne lokacin da ƙwai biyu da aka fitar a lokacin al’ada ɗaya kuma ta hadu da kwayoyin maniyyin wani mutum daban a wata haɗuwa ta daban.

A cewar mahaifiyar ‘yar shekara 19, ta haifi tagwayen watanni tara bayan ta kwanta da maza biyu a rana guda. Ta gudanar da gwaje-gwajen don sanin mahaifin yaran amma ta yi mamakin sakamakon gwajin. “Na tuna cewa na yi jima’i da wani mutum kuma na kira shi ya yi gwajin, wanda hakan ya tabbata,” matar ta ce tana neman a ɓoye sunan ta.

“Na yi mamakin sakamakon. Ban san wannan zai iya faruwa ba. Sun yi kama da juna sosai,” in ji ta. Ƙwararren likita, Tulio Franco, wanda ya tabbatar da yuwuwar lamarin amma ya yarda cewa ba kasafai ake yin sa ba ya ce: “Yana yiwuwa ya faru idan ƙwai biyu daga uwa ɗaya suka hadu da maza daban-daban.

Mista Franco ya ƙara da cewa “Jarirai suna raba kwayoyin halittar mahaifiyar, amma suna girma a cikin mahaifa daban-daban.”

Leave a Reply