Wata budurwa mai suna Blessing ta kashe jaririn da ta haifa a garin Potiskum

0
816

Daga Omale JOHN, Yobe

Wata budurwa mai suna Blessing, ƴar kimanin shekaru 20 da haihuwa, ta kashe jaririn da ta haifa ta hanyar yanka, a unguwar Nahuta dake garin Potiskum a Jihar Yobe.

Wata budurwa da ta nemi a sakaye sunanta, ta bayyana mana cewa, lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a, 2/09/2022 bayan Blessing ta je shagon ɗan garin su da take zama a gidan sa, ta karbi makulli da niyar zata je gida ta yi wanka.

Budurwar ta bayyana cewa, garin su daya da ita Blessing kuma su ƴan asalin garin Tafawa Balewa dake jahar Bauchi ne, tare da shi mutumin da take zama a gidan sa.

Ta ƙara da cewa, sun taho garin Potiskum neman sana’ar yi domin dogaro da kai da kuma tallafawa iyayen su, duba ga halin da iyayen na su ke ciki.

Wata matar ma da ba ta yarda a bayyana sunanta ba, ta ce, tun da jumawa suka gano cewa ita Blessing tana ɗauke da juna biyu amma ta musanta hakan.

Mun sami damar tuntuɓar wakilin mai unguwar Nahuta, inda ya bayyana mana takaicin da ya ji da faruwar wannan lamari.

Ya ce, rahoton ya zo musu ne da misalin ƙarfe 8:00 na yamma a ranar da abin ya faru, sun kira jami’an tsoron zuwa wurin kuma tuni aka garzaya da su asibiti inda aka tabbatar cewa jaririn ya mutu sa’anan ita Blessing aka riƙe ta agadon asibiti ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro bayan nan kuma aka yi jana’izar jaririn.

Neptune Prime ta nemi ta ji ta bakin ita Blessing domin sanin waye ne uban jaririn da ta kashe, duba da cewa ita ba matar aure ba ce kuma menene dalilin aikata wannan mummunar aika aikar, amma abin ya ci tura.

Neptune Prime ta kuma yi ƙoƙarin tuntuɓar jami’an tsaron domin sanin halin da ake ciki amma suka ce sai sun kammala bincike kafin su fidda bayanai.

Leave a Reply