Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Zaria

0
217

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da fatattakar ‘yan bindiga a yankin Fondisho da ke ƙaramar hukumar Igabi kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Laraba ta ce sojojin sun samu kwararan bayanan sirri kan maɓoyar ‘yan bindigar, kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka yi musu kwanton ɓauna.

Sai dai ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin fantsama cikin daji, amma hakan ba ta samu ba sakamakon bude wutar da jami’an tsaron Najeriyar suka yi. Sojojin sun yi nasarar kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar, sun kuma ƙwace makamai kamar bindiga da alburusai, har da tsabar kudi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da yin sintiri a yankin har sai sun tabbatar da kakkaɓe ‘yan bindigar da suka hana jihar Kaduna da jihohi maƙwabta sakat wajen satar mutane domin neman kudin fansa.

Leave a Reply