Tirƙashi! Ƙani ya Ƙwace matar yayansa a Kenya

Daga Fatima MONJA, Abuja

Wani mutum mai shekaru 56 ya bayyana irin wahalar da yake sha na kula da yara bakwai da matarsa ta bar masa bayan da ta tare da ƙaninsa a ƙasar Kenya. Simon Murefu Muyeho ya ce,” ƙaninsa ɗan acaba ne, yakan ɗauki matarsa Farida a babur har soyayya ta ƙullu a tsakaninsu. Yace, yayin da kusancinsu ya yi nisa, Farida ta bayyana soyayyarta ga ƙaninsa, wanda suka koma zama tare a kyarkashin rufi daya.

“Nakan bibiyi lamarin, nakan cewa Ƙanina ya dawo min da matata, amma ya ƙi. Duk da haka, ba zan fidda rai ba game da matata. Idan haka ya ci gaba da faruwa, zan tunkari hukumomi domin warware matsalar.”

A cewar mutumin, kullum ƙaninsa na nuna baya tare da Farida, amma a zahiri ba gaskiya bane, domin kuwa kullum akan gansu tare. Ya kuma shaida cewa, ƙanin nasa yakan sauya wuraren zama daga gari zuwa wani garin saboda kada a gane inda suke.

A martanin matar da ake rikici a kanta, a nata ɓangaren, Farida, wacce ‘yar kasuwa ce ta bayyana cewa, mijin nata na musguna mata. Ta ce: “Ya cika fada. yakan suburbuɗe ni duk lokacin da ya dawo daga aiki. Yana sana’ar gadi ne kuma yakan dawo gida ne da safe a buge bayan ya sha taba da barasa.

Ya ma kusan kashe ni, amma kwanana na gaba, saboda yana zargin ina masa kwange. “Ya taba ƙona ni, ya kuma karya min hannu. Wannan yasa nake da nakasa. Sai dai yunwa ta karmu matuƙar ban nema abin da zamu ci ba. Mutum ne mara kamun kai.”

An hana ta ganin ‘ya’yanta Farida ta kuma bayyana cewa, mijin nata ya haramta mata ganin ‘ya’ya bakwai da suka haifa tare, bayan ta zaɓi zama da ƙanin mijinta. Ta ce tana ƙaunar ƙanin mijin nata saboda ya san yadda ake tafiyar da mace da biyan buƙatun ta.

Shi kuwa ƙanin mijin Farida cewa ya yi, matar ba ta cikin kwanciyar hankali a zamanta da dan uwansa, don haka ya samu damar zama da ita.


Comments

2 responses to “Tirƙashi! Ƙani ya Ƙwace matar yayansa a Kenya”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Tirƙashi! Ƙani ya Ƙwace matar yayansa a Kenya […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Tirƙashi! Ƙani ya Ƙwace matar yayansa a Kenya […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *