No menu items!

Sample Page Title

Date:

An kama wani sojan Najeriya Lorliam Emmanuel da laifin sata da kuma sayar da harsasai ga ‘yan ta’addar Boko Haram. A cikin wani faifan bidiyo, Emmanuel, wanda aka ce yana maƙale ne da Bataliya Task Force Battalion 156, mai suna ”Operation Hadin Kai” a Mainok, jihar Borno, an kwance masa makamai, aka bincike shi kuma aka gano yana ɗauke da alburusai.

KALLI BIDIYON ANAN: https://youtube.com/shorts/X67S0GeLrhg?feature=share

Bidiyon ya nuna yadda aka cire harsashin daga wata riga da ya naɗe a kugu. An jiyo abokan aikinsa suna cewa, “Ka ga rayuwarka? Kai, za ka je ka ba Boko Haram wadannan abubuwa domin su zo su far mana a wannan sansani. Kada ku damu. Allah ya Fika.

“Duk waɗannan ba su da kyau, sun yi tsatsa,” in ji wani soja dangane da harsasai da, da alama sun kasance a hannun wanda ake zargin na ɗan lokaci.

Wanda ake zargin dan asalin jihar Binuwai ne, an ce an mika shi ga jami’an leken asirin soji domin gudanar da bincike.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...