Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa

0
94
Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa
Masarautar Haɗejawa da Katsinawa

Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa

Daga Ma’azu Hamza Hadejia

Ɗalibai suna ta min tambaya akan tarihin asalin wasan Haɗejawa da Katsinawa sai naga ya kamata yau na bada wannan amsar.

Masarautar Katsina ba makwabciyar Haɗeja bace, tana da ɗan nisa da ita, daga arewa maso yamma (Northwest). Dukkan su Habe sun mulke su kafin Jihadi ya haɗa su cikin Daular Sakkwato.

Akwai kyakkyawar danganta ta wasanni tsakanin al’umomin Masarautun guda biyu wacce ta kullu shekara da shekaru..Akwai bayanai daban-dabam da ake jingina su a matsayin dalilan da suka kawo wannan dangantakar, kuma dukkan su suna da harshen damo.

Dalili na farko an danganta shi da wasan dangi. A karkashin wannan ajin akwai kaulin da yayi bayanin cewa asalin waɗanda suka kafa Haɗejia da Katsina maharba ne.

Lokacin da suke yawan harbin su har suka kawo ga yankin Hadejia, sai wasu daga cikin su zauna zama na dindindin, saboda ganin irin ni’ima da dausayin wurin.

Ragowar sai suka zarce har suka zo yankin Katsina, suka zauna. A dalilin su jama’a ta karu har aka sami Sarauta. Duk da nisa tsakanin waɗannan ‘yan uwa, sun cigaba da mu’amala har ake ce wani ɗan Sarkin Haɗeja ya aure diyar Sarkin Katsina.

Wannan al’amari ya faru shekaru da dama kafin Jihadi, wato lokacin mulkin Habe.

Wani ƙaulin kuma yana jingina dalilin samuwar dangantakar wasannin ga Fulanin da suka Jagoranci Jihadi a yankin Haɗeja da Katsina. Wannan bayani ya nuna cewa dukkan su ‘yan uwan juna ne, kuma tare suka yi kaura zuwa yankin Katsina.

Ardo Abdure da jama’arsa sun zauna a ɓangaren Kankiya kafin daga baya su yi kaura gabas har suka iso yankin Haɗeja suka zauna. Sun cigaba da hulɗa tsakaninsu har aka yi Jihadi suka kasance shugabannin Masarautun guda biyu.

A ɗaya hannun wasu suna jingina asalin wasannin ga yaƙi tun a lokacin mulkin Habe. Wani ƙaulin yace akwai lokacin da Sarkin Katsina na wannan zamanin ya daura yaƙi zuwa Haɗeja, kafin ya ƙaraso cikin ƙasar Haɗeja ya yada zango a cikin ƙasar Gumel.

Sarkin Haɗeja ya samu labarin zuwan Sarkin Katsina, saboda haka sai ya tada wani daga cikin Jarumansa domin yaje ya gano irin shirin Katsinawa.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Wannan Jarumi na Haɗeja yayi kyakkyawan shiri ya kama hanya ya isa sansanin abokan gaba da dare. Ba tare da wani ya ganshi ba, kai tsaye ya wuce tantin Sarki ya sake shi da wata kuyangarsa suna barci..

Nan take ya kwance wandon Sarkin Katsina ya daurawa kuyangar, ya kuma cire dan kwalin kuyangar ya daurawa Sarki, a wani ƙaulin ya daidaita wuka Sarki yayi tafiyarsa ba tare da ya cutar da su ba.

Da gari ya waye Sarki ya farka yaga abin da aka yi musu, ya tabbatar ban da Haɗejawa ba mai yi masa wannan, sai ya yanke hukunci cewa lallai sunfi karfinsa. Saboda haka ya juya akalar yaƙi ya koma gida.

Wani ƙaulin kuma yace lokacin da wannan Sarki na Katsina ya iso Gumel, kan hanyarsa ta yakar Haɗejia, Sarkin Gumel ya shawarce shi da ya janye wannan aniya tasa, kuma ya yarda ya janye.

A lokacin kuma Haɗejawa sun sami labarin fitowar Sarkin Katsina har sun gama shiri tsaf suna sauraron isowarsa sai suka ji shiru.

Wani ƙaulin yace Haɗejawa ne suka tunkari Katsinawa da yaƙi, suka bi ta Daura. Yayin da suka yi kusa da Katsina, sai suka fahimci Katsinawa ba kanwar lasa bace, saboda haka suka janye suka dawo gida.

Daga waɗannan bayanai na dalilin dangantakar wasannin tsakanin Haɗejawa da Katsinawa za’a iya fahimta cewa koda akwai ‘yan uwantaka, anfi bada karfi akan dalilin yaƙin da ba’a yi shi ba.

Leave a Reply