Tarihin Rijiyar Bozundalla wadda ta yi shekaru sama dubu ba taɓa ƙafewa ba

0
241

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rijiyar Bozundalla da ke garin Wawa na ƙaramar hukumar Funakaye ta jihar Gwambe, rijiya ce mai ɗimbim tarihi da abubuwan al’ajabi. Garin Wawa, wani gari ne dake kusa da babban birnin Bajoga, hedikwatar ƙaramar hukumar Funakaye a jihar Gwambe. Daga Bajaoga za ka yi tafiyar kilomita 15, zuwa kwanar Baffaru, to a nan za ka hau mashin zuwa garin Wawa.

Garin yana lungu sosai, indai ba ranar kasuwar garin ba, to ba kasafai ake samun mota zuwa garin ba, dole sai dai a hau mashin. Idan ka hau mashin za’a yi ta falfala gudu da kai a cikin ƙungurumin daji. Duk da akwai kwalta, amma kwaltar da ita da babu duk ɗaya, domin kuwa kwaltar ta mutu murus. Haka za ku yi ta faɗa wa ramuka, manya da ƙanana. Sai kun yi tafiyar kusan awa ɗaya, kafin ku isa garin Wawa. Garin Wawa, gari ne na ƙabilun Bolawa, garin yana da matsakaicin girma da jama’a hululu.

Cikin daji za ku yi ta nausawa, amma a hanya akwai garuruwan Biri guda biyu. Wato Birin Fulani da Birin Bolawa, suna maƙwabtaka da juna.

Wakilin Neptune Prime, Ibraheem El-Tafseer ya yi tattaki har zuwa wannan gari don tattaunawa da Dagacin garin na Wawa, don jin haƙiƙanin tarihin wannan Rijiya ta Bozundalla mai ɗimbim tarihi da abubuwan al’ajabi.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya taya kiristoci murnar bikin Ista

Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance;

NEPTUNE HAUSA: Yallaɓai, da farko muna so ka gabatar da kanka a masu karatunmu?

DAGACIN WAWA: Suna na Alhaji Abubakar Sadik Lawal. Ni ne Dagacin wannan gari na Wawa.

NEPTUNE HAUSA: Muna so ka bayyana mana tarihin wannan Rijiya ta Bozundalla?

DAGACIN WAWA: Wannan Rijiya tana da tarihi mai yawan gaske, sai dai zan gutsira muku ɗan abin da ya samu. Asalin wannan Rijiya ta shafe shekaru sama da dubu kuma babu wani mutum ɗaya da zai ce shi ne ya tona ta. Sai dai an sabunta ta shekaru saba’in da suka gabata. Sakamakon zabtarewa da wani ɓangare na Rijiyar ya yi, sai Sarkin wancan lokacin, ya sa aka yi gayya irin na mutanen mu (Bolawa), aka ɗebo itacen ƙiryoyi, to waɗannan itatuwan ƙirya ɗin aka ɗaure ta, kamar yadda ka leƙa ka gani. Babu Siminti ko kaɗan da aka ɗaure ta da shi.

Asalin yadda aka samu wannan Rijiya ba mutum ba ne ya samo ta, dabba ce ta gano ta. Akwai dabba irin ta mu ta fada, wato Goɗiya (ta macen Doki). Yadda abin ya faru shi ne, ita wannan ta macen Dokin, kullum aka dawo daga kiwo aka ba ta ruwa ba ta sha. To sai wannan mai Dokin ya damu matuƙa akan me ya sa idan an ba ta ruwa ba ta sha?

To sai wannan mai Dokin ya yi wata hikima, ya ƙira wasu mutane daga fada, suka bi bayan wannan Dokin bayan ta gama kiwo. Sai aka ga ta shiga cikin wata duhuwa ta bishiyoyi, sai suka laɓe suna kallon ta. Bayan ‘yan mintuna, sai suka ga Dokin ta fito. Da suka leƙa inda ta shiga ɗin, ashe ruwa ne a kwance malala a wajen. To wannan shi ne asalin gano wannan Rijiya. Ruwan ta ƙarƙashin duwatsu yake ɓulɓulowa.

Ita wannan Rijiya tana da suna, ana ce mata Bozundalla, kalma ce ta Bolanci. Dalla ana nufin tsakiya. Bozundalla ana fassara shi da tsakiyar gari, amma ka ga inda Rijiyar take ba tsakiyar gari ba ne. Amma a wancan lokacin nan ne tsakiyar Ganuwa da Ganuwa. Tsakiyar gari ɗin kenan a wancan lokacin. Wawa tana da Ganuwa guda uku. To ka ji yadda aka samo wannan Rijiya.

NEPTUNE HAUSA: Da yake an san Rijiyoyi da ƙafewa, wasu ma sai an musu yasa, ko wannan Rijiya ta taɓa ƙafewa?

DAGACIN WAWA: Wannan Rijiya ba ta taɓa ƙafewa ba, sama da shekaru dubu. A tarihi dai mun tarar da iyayenmu da kakanninmu da iyayen kakanninmu, duk haka suka ganta, kuma haka suka tafi suka barta, ba taɓa ƙafewa ba. Amma a shekaru kamar 70 da suka gabata, an sabunta ta, saboda yau da kullum ana ɗiban ruwa a cikinta, to akwai itatuwa na sama-saman kan Rijiyar, waɗanda aka ɗaure kan Rijiyar da su, sun ciccire. Shi ne aka yi gayya, aka ƙira ‘yan’uwanmu Bolawa na nesa da na kusa, aka taru aka rufe saman Rijiyar. Aka sake shirya musu itatuwan kamar yadda suke a da can.

Ita dai wannan Rijiya an ɗaure ta ne da itatuwan ƙirya tun daga jikin duwatsun da ruwan yake ɓulɓulowa, har zuwa sama. Kuma ruwa a wannan Rijiya bai taɓa ƙafewa ba, tun daga wancan lokacin da aka gano ta har zuwa yau ɗin nan da nake hira da kai.

Wannan Rijiya tana da zurfin gaba 16, duk gugar da muke zarawa a ɗebo ruwa, tsayinsu gaba 16, kuma ba mu taɓa ƙarawa ba. Kuma awa 24 ake ana ɗiban ruwa a cikinta. Kuma za ka samu mutane sama da 50 kowa ya zara gugarsa yana ɗiban ruwa a ciki.

NEPTUNE HAUSA: Yaya daɗin wannan ruwa yake, yana da zartsi ne, ko gishiri-gishiri ko kuma kanwa-kanwa da aka san ruwan wasu rijiyoyi da shi?

DAGACIN WAWA: Ruwan wannan Rijiya, ruwa ne mai daɗin gaske. Ba don Azumi ba, da kasha ka ji da bakinka. Amma tun da ka ɗiba idan an sha ruwa za ka gaskata zance na.

Mu mun ji labari daga wajen kakanninmu cewa, wannan Rijiya tana haɗe ne da kogin Gashinge da ke ƙaramar hukumar Nafaɗa ta jihar Gwambe. Ko waye ka tambaya a yankin Nafaɗa zai nuna maka bakin rijiyar Wawa, wanda ake ce masa ‘Bobuzum Wawa’.

A wancan lokacin akwai Sarkin ruwa, da ya zo nan, ya ce kwale-kwalensa ya ɓata, kuma yana cikin wannan Rijiyar. Aka yi ta mamaki. Ya ce shi dai a ba shi izini zai shiga ya fito da kwale-kwalensa. Sarkin Wawa na wancan lokacin ya ba shi izini ya shiga. Ya shiga rijiyar shi da Karensa. To sai Sarkin ya tura mutane a kan Dawakai, a kan su je can Gashinge ɗin su jira su ga fitowarsa. Ai kuwa suna isa can, sai ga shi, sun iso tare. Sarkin ruwan sai ga shi ya fito tare da kwale-kwalensa. To wannan shi ne ya tabbatar mana da cewa wannan Rijiya tana haɗe da kogin Gashinge na ƙaramar hukumar Nafaɗa.

NEPTUNE HAUSA: Ganin yadda mutane sama da 50 suke cike a kan wannan rijiya kowa yana ɗiban ruwa, ko wani ya taɓa faɗawa wannan rijiya ya mutu?

DAGACIN WAWA: Wannan rijiya ba ta taɓa kashe kowa ba. Asali ma babu wani mutum da ya taɓa faɗawa wannan rijiya, kuma ba dare ba rana ake ɗiban ruwa a wannan rijiya, amma babu wanda ya taɓa faɗawa.

NEPTUNE HAUSA: To ko akwai wani sirri da ruwan wannan rijiya yake da shi? Ma’ana yana maganin wani abu idan an sha?

DAGACIN WAWA: (Dariya). Wannan abarwa Allah kawai. Ba komai za mu bayyana wa duniya ba.

NEPTUNE HAUSA: Akwai wani ƙalubale da kuke fuskanta game da wannan rijiya ko wannan gari?

DAGACIN WAWA: Babban ƙalubalenmu a wannan gari shi ne matsalar ruwan sha. Ka gani da idonka yadda jama’a suka yi ɗafifi suna ta ɗiban ruwa a wannan rijiya. To ita kaɗai ce take ba da ruwa, duk rijiyoyin garin sun ƙafe. Ko an tona rijiya to daga baya ƙafewa take. Wannan ce kaɗai ba ta ƙafewa, shi ya sa ka ga an mata wannan tururuwa ɗin ana ta ɗiban ruwa.

Yanzu a wannan gari, jarkar ruwa ɗaya Naira ɗari biyu ce. A ƙauyuka na kusa da mu kuwa, har Naira ɗari biyar ake sayarwa. Akwai motoci da suke zuwa garin Biri suke ɗebo ruwa a irin babban tankin nan da ake ɗorawa a saman gida, to Naira dubu 50 suke sayar da tanki ɗaya. Lallai muna fuskantar babbar matsala na rashin ruwan sha a wannan gari. Kuma hakan yana da alaƙa da yawan da jama’ar da muke da su a wannan gari, ba kamar shekarun baya ba.

Don haka muna ƙira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Gwambe, muna so a zo a inganta mana wannan rijiya mai ɗimbim tarihi, a saka ta a jerin wuraren ziyara na tarihin jihar Gwambe. Domin kuwa rijiya ce mai abubuwan al’ajabi da daman gaske. Sannan a zo samar mana da ruwan sha. Muna fuskantar matsala sosai a wannan gari na ruwan sha, kamar yadda na bayyana a baya.

NEPTUNE HAUSA: Mun gode.

DAGACIN WAWA: Ni ma na gode.

Leave a Reply